Zan Mutu Jarumi, A Gaggauta Yanke Mun Hukuncin Kisa, Sheikh Abduljabbar Ga Alkali

Zan Mutu Jarumi, A Gaggauta Yanke Mun Hukuncin Kisa, Sheikh Abduljabbar Ga Alkali

  • A Yau Alhamis, Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola na babbar Kotun Shari'a a Kano ya yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara hukunci
  • Kafin yanke hukuncin, Alkali ya waiwayi Malamin ko yana da ta cewa, yace ba ya bukatar kotu ta sassauta masa
  • Tun a watan Yuli, 2021, gwamnatin Kano ta maka Shehin Malamin a Kotu kan zargin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki SAW

Kano - A yau Alhamis, 15 ga watan Disamba, babbar Kotun shari'a a jihar Kano tace ta kama Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, da laifin ɓatanci da fiyayyen halitta SAW, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Shehin Malamin gaban Kotu kan wasu maganganu da yake yi a karatuttukansa na cin mutuncin Manzon tsira, Annabi Muhammad SAW.

Sheikh Abduljabbar Kabara.
Zan Mutu Jarumi, A Gaggauta Yanke Mun Hukuncin Kisa, Sheikh Abduljabbar Ga Alkali Hoto daga Aminiya
Asali: UGC

Da yake yanke hukunci yau Alhamis, Alkalin Kotun mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, yace, "Na gamsu cewa masu shigar da ƙara sun gama aikinsu, sun tabbatar da zargin babu waswasi."

Kara karanta wannan

'Muna Bukatar Tinubu Fiye da Yadda Yake Bukatar Mu a 2023', Jigon siyasa

Kafin bayyana hukuncin Alkali ya tambayi mai laifin cewa ko yana da abinda zai faɗa. Aminu Abubakar, lauyan wanda ake kara ya roki Kotu ta tausaya wa Malamin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai yayin da Lauyan ke kokarin nema wa Malamin sassauci, Sheikh Abduljabbar ya ƙaryata shi. Yce sam shi ba lauyansa bane kuma baima san shi ba.

"Bansan shi ba, karon farko kenan da na taɓa ganin shi, ba zai yi magana a madadi na ba, a barni na yi magana da kaina," inji shi.

Bidiyon abinda ya faru a lokacin

Kalaman Sheikh Abduljabbar gabanin yanke masa hukunci

A ruwayar Aminiya, Abduljabbar ya ƙara da cewa:

"Mai Shari'a, bayan na saurari yadda ka murɗe shaidun da na kawo, ƙa sauya duk abinda na faɗa, ka laƙaba mun kalaman da ban faɗa ba, ka yanke hukuncinka bana bukatar a sassauta mun."

Kara karanta wannan

Kano: Abubuwan da ya Dace Ku Sani Game da Sheikh Abduljabbar Kabara

"Bana bukatar kai Ibrahim Sarki Yola ka mun sassauci, a wurin Allah kaɗai nake neman sassauci. Ina son a hanzarta zartar da hukunci a kaina."
"Ina amfani da wannan dama wajen ba mabiyana hakuri su sani zan yi mutuwa ta girma, zan isa lahira da girma, iya abinda zan ce kenan Assalamu Alaikum."

A wani labarin kuma mun kawo muku yadda aka girke jami'an tsaro a harabar yankin da Kotu take domin kammmala zaman cikin aminci

Malamin ya isa harabar ɗakin zaman Kotun mintuna kaɗan kafin cikar karfe Tara na safe tare da rakiyar Dakarun gidan gyaran hali.

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta maka Sheikh Abduljabbar a gaban Kotun tun a watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262