Gwamnatin Kano Ta Fara Aiwatar Da Umurnin Kotu Kan AbdulJabbar

Gwamnatin Kano Ta Fara Aiwatar Da Umurnin Kotu Kan AbdulJabbar

  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta fara aiwatar da umurnin da kotun shari'a ta yiwa Abduljabbar
  • Yanzu dai saura kwanaki 20 wa'adin damar daukaka karar da kotun ta baiwa Malam Abduljabbar
  • Kotun a kimanin makonni biyu da suka gabata ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta fara aiwatar da umurnin da Alkalin kotun shari'a, Ibrahim Sarki-Yola yayi kan Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara.

Legit Hausa ta ruwaito muku hukuncin da Ibrahim Sarki-Yola ya yanke kan AbdulJabbar ranar 15 ga watan Disamba bayan kama shi da laifin batanci ga Manzon-Allah (SAW) a wa'azozinsa.

Bayan hukuncin kisa da aka yanke masa, Alkalin ya bada umurnin rufe Masallatansa, makarantarsa, kuma a daina sanya karatukansa a gidajen rediyo da talabijin.

Hakazalika ya umurci kwashe littafansa guda 189 kuma a gurfanar gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Masallatan sun hada da na Filin Mushe da Sharada.

Abduljabbar
Gwamnatin Kano Ta Fara Aiwatar Da Umurnin Kotu Kan AbdulJabbar Hoto: BBCHausa
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Nigerian ta ruwaito cewa a ranar Juma'a, gwamnatin jihar ta aiwatar da da wadannan umurni.

An tattaro cewa tuni an rufe Masallatan Malam AbdulJabbar biyu kuma jami'an tsaro sun mamaye wajen.

Hakazalika, an kwashe takardunsa 189 kuma an mayar da su dakin ajiya littafan gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel