Shugaban Majalisa Ya Fadi Wanda Ya 'Jawo' Tabarbarewar Tattalin Arziki Lokacin Buhari
- Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya yi jawabi kan matsalar tattalin arziki da ta addabi kasar
- Sanata Akpabio ya ce dukkan matsalolin da ake ciki yanzu suna da nasaba da irin tsare-tsaren da, Godwin Emefiele ya kawo
- Ya kuma kara da cewa a yanzu haka shugaba Bola Tinubu ya dukufa wajen samo mafita ga dukkan matsalolin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Shugaban majilisar dattijai ta kasa, sanata Godswill Akpabio, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kara hakuri da mulkin shugaba Bola Tinubu.
Shugaban majalisa ya jefa zargi kan Emefiele
Sanata Akpabio ya ce a halin yanzu shugaba Bola Tinubu yana kokarin farfaɗo da tattalin arzikin kasar ne wanda hakan yana bukatar juriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani rahoton da jaridar Leadership ta fitar, shugaban majalisar ya ce tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya lalata tattalin arzikin kasar.
Ya ce dukkan matsala da Najeriya ta samu kanta a ciki yana da alaka da irin aikin da Emefiele ya gudanar a babban bankin kasa.
Kokarin da shugaba Bola Tinubu yake yi
A cewarsa, a yanzu haka shugaba Tinubu ya dukufa wurin gina Najeriya a kan tsarin tattalin arziki mai mai dorewa, cewar jaridar Tribune Online
Har ila yau shugaban majalisar ya kara yin albishir ga 'yan Najeriya cewa lalle kokarin da Tinubu yake yi zai kai ga tudun tsira.
A cewarsa, kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya fitar da jihar Lagos daga matsalar tattalin arziki haka zai fitar da Najeriya ma.
Ya kara da cewa shugaban kasa da mataimakinsa, sanata Kashim Shettima, da ma shi shugaban majalisar suna da gogewa a harkar shugabanci da za su iya sharewa 'yan Najeriya hawaye.
Kiran Akpabio ga gwamnan Akwa Ibom
A cikin jawabin nasa, sanata Akpabio yi kira ga gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, da ya hada kai da sauran hukumomi domin cin moriyar ayyukan gwamnatin tarayya.
Babban jan hankalin da ya yiwa gwamnan shine cewa a matsayinsa na fasto ya kamata shugabancinsa ya zama cike da adalci da tsari.
Jawabin Gwamnan Akwa Ibom
A nasa bangaren, gwmana Umo Eno ya yi godiya ga shugaban kasa Tinubu wurin tabbatar da cewa jihar Akwa Ibom ta samu shugabancin majalisar Najeriya.
Ya kuma kara da cewa duk da bambancin jam'iyyar siyasa za su yi aiki tare domin kawo cigaba a jihar Akwa Ibom dama Najeriya baki daya.
Akpabio ya magantu kan masu zanga-zanga
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio ya yi zargin cewa akwai wasu tsiraru a gefe da ke ɗaukar nauyin masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Shugaban majalisar dattawan ya ce mafi akasarin mutanen da ake amfani da su wajen zanga-zangar ba su san kokarin da FG ke yi ba wajen shawo kan matsalar kasar.
Asali: Legit.ng