Rahoto: Yadda Likitan Boge Ke Zubar da Ciki Ga ’Yan Mata a Filato Kan N5,000

Rahoto: Yadda Likitan Boge Ke Zubar da Ciki Ga ’Yan Mata a Filato Kan N5,000

  • Wani bincike ya nuna yadda wani “likitan boge” mai suna Ali Madida ya ke zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos
  • An kuma zargi Madida, da kashe wata budurwa, Halima, a wajen zubar mata da ciki da kuma jefa 'yan mata a harkar karuwanci a yankin
  • Wata 'yar jarida mai zaman kanta daga Kano ce ta tattara rahoton tare da tallafi daga Cibiyar Rediyon Mata da Gidauniyar MacArthur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jos, jihar Plateau - Wani rahoto na bincike ya nuna yadda wani likitan boge ya zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos, babban birnin Plateau.

Kara karanta wannan

Sabani ya barke tsakanin 'yan awaren Biafra da ke fafutukar a tsaga Najeriya gida 2

Wata 'yar jarida mai zaman kanta daga Kano, Ramatau ce ta tattara rahoton tare da tallafi daga Cibiyar Rediyon Mata da Gidauniyar MacArthur.

An gano likitan boge da ke zubar wa 'yan mata ciki a Jos, jihar Plateau
Bincike ya gano wani likitan boge da karbar N5,000 yana zubar wa 'yan mata ciki. Hoto: Nadzeya Haroshka / Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton ya bayyana yadda mazauna yankin ’Yan Doya ke dafifin zuwa wajen wani Ali Madida da ake zargi da gudanar da aiki a wata haramtacciyar cibiyar kiwon lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Madida na jefa 'yan mata a karuwanci

An kuma zargi Madida da jefa ‘yan matan da ya zubar wa ciki zuwa harkar karuwanci da sunan samar musu da abin dogaro da kai, jaridar The Cable ta ruwaito.

Rahoton ya ce yawancin 'yan mata da ke kasa da shekaru 15 na shiga harkar karuwanci ne saboda "talauci, jahilci da rashin kulawar iyaye" a cikin garin.

Rahoton ya ce, ‘yan matan da suka ziyarci asibitin suna haduwa da mazan da ke biyansu Naira 5,000 domin yin lalata da su.

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Lauya ya ja hankalin gwamnati kan hana dalibai masu hijabi rubuta UTME

Rahoton ya ce ana tilasta wa ‘yan matan komawa asibitin domin a zubar da cikin a idan suka samu juna biyu kuma ana karbar Naira 5,000 na aiki.

Yadda Madida ya yi ajalin Halima

A cikin rahoton, wata majiya mai suna Khadija ta ce ta ziyarci asibitin tare da kawarta Halima domin zubar da cikin.

Yayin da Khadija ta tsira daga tiyatar, kawarta ta rasu bayan ta fuskanci wasu matsaloli yayin da ake tiyatar.

“Bayan wasu watanni, na lura cewa ina da ciki, sai na koma wurin Dr. Ali inda ya cire mun. Na yi fama da ciwon ciki na tsawon watanni. Na kusa mutuwa kafin na samu lafiya.
“Bayan ‘yan watanni, wata kawata, Halima, ta je wurinsa domin ta zubar da cikinta, amma a yayin aikin zubar da cikin ne aka samu matsala, ta mutu.”

Rahoton ya ce jami’an tsaro sun kama Madida sau da dama amma daga baya a sake shi.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar jarumin dan sanda Abba Kyari ta rasu, an shirya jana'izarta a Borno

Hukumomi za su kwace lasisin Madida

Da take magana yayin taron manema labarai kan rahoton binciken, Toun Sanaiya, babbar jami’ar gudanarwa ta Cibiyar Rediyon Mata, ta yaba wa 'yar jaridar saboda “bajinta da jajircewa” wajen bankado laifuffukan.

Jami’in kula da ayyukan cibiyar, Taiwo Adeleye, ya ce hukumomin da abin ya shafa sun ba da tabbacin cewa za a kama Madida kuma za a kwace lasisinsa.

Adeleye ya kara da cewa an gano Madida har ya riga ya sake fasalin "asibitin da ba a yi wa rajista ba".

Kalli bidiyon rahoton a nan kasa:

s

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.