Ciki 15 na zubar saboda mijina, yanzu kuma yana son sakina - Matar aure ga kotu

Ciki 15 na zubar saboda mijina, yanzu kuma yana son sakina - Matar aure ga kotu

Wata ma'aikaciyar jinya 'yar asalin Ibadan mai suna Sukurat Adewale, cike da hawaye a ranar Juma'a ta sanar da wata kotun gargajiya a garin Ibadan da ke jihar Oyo, mummunan halin da take ciki tare da mijinta.

Ta zargi mijinta mai suna Adewunmi Adewale da sanya ta zubar da ciki har 15 wanda ta dauka, amma daga bisani sai ya barta tare da yaranta uku a gidan haya ba tare da kula ba.

Sukurat ta ce bincikenta ya nuna cewa Adewale ya auri wasu mata biyu daga wurare daban-daban a garin Ibadan, kuma ta roki kotun da ta bata rikon 'ya'yansu uku.

Sukurat wacce take martani a kan bukatar sakin da Adewale ya mika gaban kotun, ta ce mijinta ya saba barinsu sai ciwo ya samesa ya dawo mata gida.

Ta ce, "Bana son ci gaba da zaman aurena. A zatona mijina zai sauya hali tun bayan da ya kwashe shekaru biyu baya tare da mu kuma ya dawo na karbeshi.

"Ya dawo da rashin lafiya kuma nayi doguwar jinyarsa. Na kai wa iyayensa kara amma bai sauya hali ba. Na yi azumi da addu'o'i amma duk da haka shaidancinsa ba ya karewa.

"Sau 15 yana dirka min ciki kuma ina zubarwa saboda baya so. Karon karshe da ya bar gida shine lokacin da ya bukaci in zubar da cikin tagwayen da na haifa.

"Har yanzu ina gidan hayar da ya bar ni. Iyayena ne suka rokesa da ya dawo saboda mutuncinsu saboda basu son in fara neman maza.

Ciki 15 na zubar saboda mijina, yanzu kuma yana son sakina - Matar aure ga kotu
Ciki 15 na zubar saboda mijina, yanzu kuma yana son sakina - Matar aure ga kotu. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Dole ne a sake zabar Donald Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden

“Ni kadai nake kula da 'ya'yana. A ranar da ya bukaci in kaiwa iyayensa yaranmu su gaisa, ya je daga baya ya daukesu ba tare da tunanin halin da za su fada ba.

"Da kyar dattawa suka shawo kansa sannan na sake ganin yarana. Ya kwashe dukkan kayansa daga gidan saboda auren wasu mata biyu da yayi. Daya daga cikinsu ta haifa masa yara biyu."

A korafin da mai kawo karar ya mika wa kotun, ya bayyana cewa yana son sakin Sukurat saboda fitinanniya ce, bata jin magana, ga ta da bakar mugunta.

Ya sanar da kotun cewa, "Tana barazanar kasheni da kanta a lokuta masu yawa. Na bar gida saboda muguntarta. Tana zagin iyayena a duk lokacin da ta so.

'Ta saba zuwa wurin bokaye, malamai da fastoci. Da gaske ina dukanta idan raina ya baci, amma ina kula da ita. Tana fatan ta ga na bar aiki. Ta taba gayyatar 'yan sanda suka kama ni tare da kulle ni na kwanaki biyu."

Alkalin kotun, Ademola Odunade, ya tsinke igiyar auren tare da ba mijin rikon dansu mai shekaru 15. Sauran biyun kuwa ya bai wa mahaifiyar.

Odunade ya bai wa Adewale umarnin biyanta N10,000 a kowanne wata domin kula da yaran biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel