Kasashen da aka fi zub da ciki a Duniya, leka kuga Najeriya ko ta nawa ce

Kasashen da aka fi zub da ciki a Duniya, leka kuga Najeriya ko ta nawa ce

- Ghana da Najeriya ne kasashen da aka fi binciken kwayoyin, kamar yanda alkalumman Google suka nuna

- A Ghana ana bada damar zubar da ciki ne Idan anyi wa mace fyade ko don ceto rayuwa

- Haka ma a Najeriya, dokar kasar ta bada dama ne a zubar da ciki in har rayuwar mace na cikin hatsari

Kasashen da aka fi zub da ciki a Duniya, leka kuga Najeriya ko ta nawa ce
Kasashen da aka fi zub da ciki a Duniya, leka kuga Najeriya ko ta nawa ce

Yadda ake binciken magungunan zubar da ciki a Google a shekaru 10 da suka shude, ya nunka, a binciken da BBC ta gabatar.

A binciken an gano cewa anfi binciken kwayoyin a yanar gizo ne a kasashen da aka haramta zubar da ciki.

Mata sun koma amfani da hanyoyin fasaha gurin zubar da ciki ta hanyar da yada bayanan likita ta kafafen sada zumunta.

A yanzu wannan itace hanyar zubar da ciki da zamani yazo da ita.

A kasashen duniya da aka sanya tsauraran dokoki, na sai dai don ceto ran mace ne ake zubar da ciki ko kuma aka haramta baki daya, anfi binciken kwayoyin fiye da kasashen da babu wata doka.

Hanyoyi biyu ake amfani dasu gurin zubar da ciki: Tiyata da Magani.

Zubar da ciki ta hanyar shan magani ya shafi shan magunguna irin su Misoprostol da Mifeprostone, wanda in har an sha zai sa ciki ya zube.

Kamar a Birtaniya, likitoci ne ke rubuta maganin amma a kasashe da ake da dokar, ta yanar gizo ake bincika don gujewa hukunci.

DUBA WANNAN: An tona sirrin masu kokarin hana dimokuradiyya tun Abiola

Ghana da Najeriya ne kasashen da aka fi binciken kwayoyin, kamar yanda alkalumman Google suka nuna.

A Ghana ana bada damar zubar da ciki ne Idan anyi wa mace fyade ko don ceto rayuwa.

Haka ma a Najeriya, dokar kasar ta bada dama ne a zubar da ciki in har rayuwar mace na cikin hatsari.

Kasashe 25 na duniya da aka fi binciken kwayoyin zubar da ciki, 11 daga ciki kasashen Afirka ne, 14 kuma a Latin Amurka.

Dukkaninsu kuma sun haramta zubar da ciki ko kuma sun yarda ne in rayuwar mace na cikin hatsari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel