Likita ya kashe yarinya sanadiyar zub da ciki (Hoto)

Likita ya kashe yarinya sanadiyar zub da ciki (Hoto)

Hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke wani likita mai suna, Dakta Olawale Raji, da wata ma’aikaciyar kula, Funmilayo Olusegun, kan laifin zubarwa wata budurwa mai suna Aminat Atisola, ciki wanda ya zama ajalinta.

A wata jawabin da kakakin hukumar yan sanda, Abimbola Oyeyemmi, ya saki, ya ce an damke litikan da ma’aikaciyar ranan Alhamis, 26 ga watan Yuli ne bayan wata Bose Kazim, wacce yar uwar marigayiyar ta kai kara ofishin yan sanda.

Bose tace Aminat na da cikin wata biyu kuma ta nemi likitan asibitin ya zubar mata da ciki. Likita ya tafi gidanta tare da ma’aikaciyarsa domin aiwatar da wannan abu.

Jim kadan bayan tiyatan, Aminat ta fara rashin lafiya har ta cika. An yi kokarin kai babban asibitin Abeokuta amma ta mutu a hanya.

An kai gawarta dakin ajiye gawawwakin asibitin State general da ke Ota, jihar Ogun domin gudanar da bincike. Ba da dadewa ba za’a kai likitan sashen gudanar da binciken hukumar domin gudanar da bincike da hukunawa.

Kakakin ya kara da cewa zubar da ciki haramun ne a kundin tsarin mulkin Najeriya kuma duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel