Isra'ila Za Ta Rufe Gidan Talabijin Na Aljazeera a Kasarta
- Yayin da ake ci gaba gumurzu a Isra'ila, gwamnatin kasar ta shirya rufe gidan talabijin na Aljazeera a ƙasar
- Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu shi ya tabbatar da haka inda ya ce za su kwace kayan aikinsu a kasar
- Gwamnatin kasar na zargin gidan talabijin din da ke kasar Qatar da ruruta wutar rikicin da goyon bayan Hamas
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Isra'ila - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa za ta rufe gidan talabijin na Aljazeera.
Netanyahu ya zargi gidan talabijin din na kasar Qatar da kara ruruta wutar rikici a kasar Isra'ila wurin goyon bayan Hamas.
Wane mataki Isra'ila ta dauka kan Aljazeera?
Fira Ministan ya bayyana haka ne a yau a shafinsa na X inda ya ce zai kawo karshen matsalar da suke da Ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gwamnati ta amince da rufe tashar Aljazeera da ke ruruta wutar rikici a Isra'ila."
- Benjamin Netanyahu
Netanyahu ya ce wakilan Aljazeera sun kara lalata tsaron kasar inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a rusa masu goyon bayan Hamas a cikin kasar.
Isra'ila ta zargi Aljazeera da son Hamas
Har ila yau, Ministan Sadarwa a Isra'ila, Shlomo Karhi shi ma ya bayyana goyon bayansa kan daukar matakin.
Shlomo ya ce babu wani 'yancin fadan albarkacin baki ga masu goyon bayan Hamas a rikicin Isra'ila.
"Babu batun 'yancin fadan albarkacin baki ga wadanda ke yabon Hamas a Isra'ila."
"Za mu rufe Aljazeera da gaggawa kuma za mu kwace dukkan kayayyakinsu."
- Shlomo Karhi
Turkiyya ta yanke alaka da Isra'ila
Kun ji cewa shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan, ya sanar da dakatar da harkokin kasuwanci da kasar Isra'ila.
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta ce daukan matakin yana da alaka da musgunawa Falasɗinawa da Isra'ila ke yi.
Kasar Turkiyya dama ta kasance cikin jerin ƙasashen da suke nuna wa Isra'ila yatsa tun fara kai hare-haren da ta yi zuwa Gaza a watan Oktoban shekarar 2023.
Asali: Legit.ng