Jami'an DSS Sun Hallaka Matashi Yayin Bin Layi a Gidan Mai? Hukuma Ta Yi Martani
- Hukumar tsaro ta DSS ta musanta kisan wani matashi a Legas yayin turmutsu wurin bin layin gidan mai a yankin Obalande
- Jami'an sun ce babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yaɗawa kan kisan matashin inda ta bukaci a tuntubi 'yan sanda
- Hakan ya biyo bayan hallaka matashin da wasu jami'an tsaro biyu suka yi bayan ya ƙi amincewa su shiga gabansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Hukumar DSS ta yi martani kan zargin jami'anta sun hallaka wani matashi yayin bin layin shan mai a jihar Legas.
Hukumar ta musanta cewa jami'anta ne suka hallaka matashin inda ta bukaci 'yan sanda su yi kwakkwaran bincike kan lamarin.
DSS da musabbabin kisan matashin a Legas
Wannan ya biyo bayan kisan wani matashi a Legas yayin gumurzu bayan wahalar mai da ake fama da shi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta DSS ta yi martanin ne a shafinta na X inda ta ke musanta cewa jami'anta sun yi ajalin matashin.
"Labarin cewa jami'an DSS biyu sun yi ajalin wani matashi a gidan mai a Obalande da ke Legas ba gaskiya ba ne."
"Ya kamata a tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a Legas domin samun karin bayani."
- Hukumar DSS
Martanin 'yan sanda kan kisan matashin
Daga bisani kakakin rundunar a Legas, Benjamin Hundeyin ya ce sun gano jami'in dan sanda da zargin aikata laifin.
Vanguard ta tabbatar da cewa Hundeyin ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 2 ga watan Mayu a Legas.
"Wanda ake zargi da harbin an gano jami'in dan sanda ne da ke sashen Special Protection Unit a Lion Building da ke Legas."
"Tuni aka ƙaddamar da bincike domin gano gaskiya, sannan Kwamishinan 'yan sanda ya na ganawa da iyalan marigayin domin tabbatar da adalci a binciken."
- Benjamin Hundeyin
DSS sun bindige matashi a gidan mai
A wani labarin, ana zargin wasu jami'an DSS biyu sun yi ajalin wani matashi yayin bin layin shan mai a jihar Legas a ranar Laraba 1 ga watan Mayu.
Matashin mai suna Toheeb Eniasa ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ki amincewa jami'an sun shiga gabansa inda ya bukaci su bi layi.
Asali: Legit.ng