Badakalar N80bn: Abin da Wasu Tsofaffin Gwamnoni Ke Cewa Game da Yahaya Bello
Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan abin da ya biyo bayan yunkurin da hukumar EFCC ta yi na kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wasu jami’an ‘yan sanda da magoya bayan tsohon gwamnan ne suka kawowa jami’an EFCC cikas a yayin da suka je kama Yahaya Bello a gidansa da ke Abuja.
Sama da sa’o’i 10 tsohon gwamnan ya kasa fita daga gidansa har sai da magajinsa Ahmed Usman Ododo ya kai masa dauki, wanda kuma ake zargin ya taimaka wa Bello ya tsere.
EFCC na tuhumar Yahaya Bello
EFCC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, inda ita ma hukumar DSS ta saka sunan shi a jerin wadanda za ta sakawa ido.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na shirin gurfanar da tsohon gwamnan gaban kuliya bisa zarge-zarge 19.
Zarge-zargen sun hada da halasta kudaden haram, cin amana, da karkatar da wasu kudade da suka kai Naira biliyan 80.2.
Shugaban EFCC ya yi babbar barazana
A halin da ake ciki, Ola Olukoyode, ya sha alwashin ajiye mukaminsa na shugaban hukumar EFCC idan har ba zai iya gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya ba.
Olukoyode ya kara da cewa gwamnatin sa za ta tabbatar da cewa duk wadanda suka kawo wa hukumar cikas a hukunta Bello sun fuskanci fushin doka.
Wasu tsofaffin gwamnoni sun magantu
Sai dai wasu tsofaffin gwamnoni sun soki matakin da Yahaya Bello ya dauka na kin yarda a kama shi da kuma kin mutunta tsarin doka.
1. Adams Oshiomhole
Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo kuma wanda ya taba zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi Allah-wadai da yunkurin tsohon gwamnan jihar Kogi na kaucewa kamu.
Oshiomhole ya kuma yi Allah-wadai da matakin da Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya dauka na kare magabacinsa daga shiga hukumar EFCC.
Kalli bidiyon Oshiomhole a nan kasa:
2. Samuel Ortom
Tsohon gwamnan jihar Benuwe shi ne na biyu a jerin tsofaffin gwamnoni da suka yi tur da Yahaya Bello, wanda kuma ya zargi tsohon gwamnan na Kogi da laifin cin zarafin doka.
A wani taro da mai taimaka masa ya shirya a Makurdi, babban birnin jihar Benue, Ortom ya yi kira ga Bello da ya fito daga inda ya boye ya amsa tambayoyi a gaban hukumar EFCC.
Ortom, jigo a jam’iyyar PDP, ya ci gaba da cewa, abin da Yahaya Bello yake yi tamkar tozarci ne ga kungiyar tsofaffin gwamnoni, in ji rahoton jaridar Premium Times.
Yahaya Bello: AISA ta tuntubi EFCC
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa makarantar kasa-da-kasa ta Amurka da ke Abuja (AISA) ta tuntubi hukumar EFCC kan kudin makarantar 'ya'yan Yahaya Bello.
A cewar makarantar AISA, Ali Bello, yaron tsohon gwamnan jihar Kogi ya turawa makarantar $845,852 a ranar 7 ga watan Satumba, 2021, inda ta nemi ta mayarwa hukumar kudaden.
Asali: Legit.ng