Darajar Naira Ta Kuma Sauka Kasa, Farashin Dalar Amurka $1 Ya Dumfari N1,405

Darajar Naira Ta Kuma Sauka Kasa, Farashin Dalar Amurka $1 Ya Dumfari N1,405

  • Darajar Dalar Amurka tana ci gaba da karuwa a kasuwar hada-hadar kudi yayin da ta haura zuwa N1,402/$1 a ranar Alhamis
  • Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa, darajar Naira ta ragu da N12 daga N1,390 da aka rufe cinikinta a ranar Talata
  • Ana ce Naira ta yi wannan faduwar ne biyo bayan karancin Dalar Amurka da aka samu a kasuwanin hukuma da na bayan fage

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Naira ta sake faduwa kasa a kasuwar gwamnati, inda ta koma N1,402 idan aka kwatanta da Dalar Amurka a ranar Alhamis.

Bayanai daga shafin kamfanin musayar kudi na FMDQ sun nuna cewa, darajar Naira ta ragu da N12 ko kuma kashi 0.86% daga N1,390 da aka rufe cinikinta a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

Darajar Naira da Dala a Najeriya
Darajar Naira ta fadi a kan Dalar Amurka a kasuwar canji a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ba a bude kasuwar hada-hadar kudin a ranar Laraba ba saboda bikin ranar ma'aikata, a cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin faduwar darajar Naira

A kasuwar canji ta Najeriya mai cin gashin kanta, Naira ta haura zuwa N1,445 a ranar Alhamis, amma ta fadi zuwa N1,299 kafin aka rufe cinikinta a N1,402 a ranar.

An samu karuwar hada-hadar dala a NAFEX da kashi 3.1% ko $7m zuwa $232 a ranar Alhamis daga $225.36m da aka yi hada-hadarta a ranar Talata.

An ce Naira ta yi wannan faduwar ne biyo bayan karancin Dalar Amurka da aka samu a kasuwanin hukuma da na bayan fage.

N1,360/$1 a kasuwar canji (BDCs)

Hakazalika, 'yan kasuwar canji (BDCs) sun ce darajar Naira ta sauka kasa a hada-hadar da aka yi a ranar Alhamis.

Abubakar Yahu, wani dan canji a Wuse 2, Abuja, ya ce ’yan kasuwa sun sayi Dala kan N1,310 kuma sun sayar da ita kan N1,360 inda suke bin ribar N50.

Kara karanta wannan

Ana murna yayin da Naira ta sake farfaɗowa, ta yunƙuro da 1.98% a kasuwa

Ya ce darajar Dala tana karuwa saboda yawan bukatar ta da ake samu amma bai kai na lokacin da Naira ta koma N1,900 a watanni biyu da suka wuce ba.

$1 za ta iya faduwa kasa da N1,000

A wani rahoton Legit Hausa, kamfanin rukunin Goldman Sachs ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta kara tashi sama yayin da Dalar Amurka za ta karye zuwa kasa da N1,000/$1.

Tun da fari dai masana sun ce $1 za ta dawo N1, 200 zuwa karshen 2024, amma dabarun CBN sun jawo yanzu ana ganin Naira za ta iya fin haka kafin shekarar ta kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.