Da Gaske Gwamnatinmu za ta Yaki Cin Hanci, Kashim Shettima ya Ba 'Yan Najeriya Tabbaci

Da Gaske Gwamnatinmu za ta Yaki Cin Hanci, Kashim Shettima ya Ba 'Yan Najeriya Tabbaci

  • Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce da gaske za ta yi yaki da cin hanci da rashawa ba tare da nuna son kai ba
  • Mataimakin Shugaban kasar, Kashim Shettima ne ya bayyana matsayar gwamnatin a wani taron tattauna kudirin ci gaban tattalin arzikin gwamnatin
  • Daga wadanda su ka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da hukumar EFCC ke tuhuma da almundahanar sama da N80bn

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu ba za ta nuna sani ko sabo ba a yakin da take yi da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kwana 7: kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnati wa'adin janye karin kudin wuta

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a Alhamis yayin wani taro kan yadda kudurorin gwamnatin Tinubu za su warware matsalar da Najeriya ke ciki.

Najeriya ta ce ba za ta daga kafa a kan cin hanci da rashawa ba
Mataimakin shugaban kasar na wannan batu ne yayin da Yahaya Bello ke zaune ya na ji Hoto:@KashimSM
Asali: Twitter

Alhaji Kashim Shettima na wannan batu ne yayin da Yahaya Bello ke zaune a wurin taron, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima bai sakaya matsayarsu ba

Duk da kasancewar Yahaya Bello, tsohon Gwamnan APC a jihar Kogi a wajen taron, hakan bai sa mataimakin shugaban kasar sakaya matsayarsu kan almundahana a kasar nan ba.

Yahaya Bello dai na fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da wawashe kudi daga baitul-malin jihar Kogi lokacin ya na gwamna.

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC na zargin tsohon Gwamnan da almundahanar sama da Naira Biliyan 80.

Manufar gwamnati kan yaki da rashawa

Amma a cewar Kashim Shettima, gwamnatin tarayya ba za ta nuna sanayyya a yakin da ta ke yi da masu rugurguza tattalin arzikin kasa ba, kamar yadda Naija News ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai jiga-jigai a jam'iyyar APC da a yanzu haka ke fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci.

Daga cikinsu akwai tsohon Gwamnan Kano, kuma shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, da tsohon Gwamna Nasir El Rufa'i na jihar Kaduna.

Yahaya Bello ya musanta gayyatar EFCC

Mun ruwaito mu ku a baya cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya musanta ikirarin da hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na cewa ta mika masa goron gayyata.

Ofishin Yahaya Bello ya ce sam babu gaskiya cikin batun, domin hukumar EFCC ba ta taba rubuto musu cewa ta na bukatar tsohon gwamnan ya bayyana gabanta ba kan zargin cin hanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.