Fadan Daba: Fusatattun Matasa sun Cinnawa Kasuwa Wuta a Lagos

Fadan Daba: Fusatattun Matasa sun Cinnawa Kasuwa Wuta a Lagos

  • Ana arangama tsakanin wasu 'yan daba a yankin Ile-Epo da ke jihar Lagos wanda ya janyo asarar dukiya da dama, babu rahoton asarar rai
  • Rahotanni sun ce tun a daren jiya aka fara samun hatsaniya tsakanin 'yan dabar, kuma rashin cimma maslaha ya juyar da lamarin zuwa kazamin fada
  • Shaidun gani da ido sun ce lamarin na neman ya gagari jami'an tsaro, domin babu abun da ake ji sai ihu da fashewar gilasai da hayaki daga wutar da ke ci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- 'Yan daba sun yi arangama a wata kasuwa da ke jihar Lagos, wanda ya kai ga raunata mutane da dama, sai dai har yanzu babu tabbacin asarar rai.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: An yi ram da 'yar sanda bisa zarginta da satar yara a Sokoto, an ceto yara 5

'Yan dabar sun kona shaguna da dama yankin Ile-Epo na jihar ta Lagos tare da yi wa juna raunuka bayan sun kwana suna hayaniya.

'Yan dabar sun kona kasuwa
Fadan da aka fara tun daren Laraba, yanzu haka ya rikide zuwa mummunan arangama tsakanin 'yan daba Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa tun a daren Laraba aka fara samun sabani tsakanin 'yan dabar, wanda ba a samu yin sulhu ba har wayewar yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rigimar ta gagari 'yan sanda

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa wurin ya runcabe, yayin da ake kazamin fada tsakanin 'yan dabar da su ke kokarin kone kasuwar.

Wani da ya nemi a sakaye sunansa ya ce:

"Wurin ya hargitse, hayaki ta ko'ina, ba abun da ka ke ji sai ihun mutane da fashewar gilasai."

Majiyar ta kara da cewa:

"Lamarin ya fi karfin gan sanda."

Punch News ta ruwaito cewa hatta jami'an kwana-kwana wurin ya gagaresu shiga, saboda ruwan duwatsu da 'yan dabar su ka yi wa motocin da ke kokarin kai agajin kashe wutar.

Kara karanta wannan

"Sako ga masarautar Zamfara": 'Yan bindiga sun saki bidiyon hadimin sarki da suka sace

Kazamin rikicin da yadda 'yan dabar su ka yi musu ca ya sa motar ta yi gaggawar juyawa, kamar yadda shaidun gani da ido su ka zayyana.

An tafka asara a gobarar kasuwar Balogun

Mun kawo mu ku cewa wata mummunar gobara ta lakume dukiyoyin biliyoyin Naira kasuwar Balogun da ke jihar Lagos, wanda hakan ya jefa jama'a cikin rudani.

Ibrahim Farinloye, shugaban hukumar bayar da agaji ta kasa (NEMA) ya tabbatar da cewa gobarar ta yi gagarumar barna, domin ta kone sassan sayar da kayan kwalliya a kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.