"Rikicin Iran da Isra'ila Ne Sila": IPMAN Ta Wanke Kanta Kan Matsalar Mai, Ta Faɗi Mafita

"Rikicin Iran da Isra'ila Ne Sila": IPMAN Ta Wanke Kanta Kan Matsalar Mai, Ta Faɗi Mafita

  • Yayin da ake fama da matsalolin man fetur a Najeriya, kungiyar IPMAN ta bayyana babban dalilin rashin mai a ƙasar
  • Sakataren kungiyar a Najeriya, James Tor ya tabbatar da cewa rikicin Iran da Isra'ila ne silar rashin man a kasar
  • Wannan na zuwa ne yayin ake fama da matsalar wahalar mai da kuma tsada a fadin kasar baki daya a 'yan kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar dillalan mai a Najeriya (IPMAN) ta ce rikicin Iran da Isra'ila ne silar matsalar da aka shiga na man fetur a kasar.

Sakataren kungiyar a kasar, James Tor shi ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu.

Kara karanta wannan

Kwana 7: kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnati wa'adin janye karin kudin wuta

IPMAN ta zargi rikicin Iran da Isra'ila ta jawo wahalar mai a Najeriya
Kungiyar IPMAN ta ce rikicin Iran da Isra'ila ne silar wahalar mai a Najeriya. Hoto: @nnpclimited.
Asali: Twitter

Mene musabbabin wahalar mai a Najeriya?

James ya ce rikicin ne ya haddasa rashin mai din da kuma yawan layi a gidajen mai da ake fama da shi a Najeriya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Najeriya ce ke shigo da mai tare da rarrabawa ga dillalan man a kasar.

Sai dai ya ce rikicin Gabas ta Tsakiya ya kawo cikas wurin samar da mai din wanda ya yi sanadin wahalhalun da ake sha a yanzu.

Kokarin NNPCL kan matsalar mai

'Dan kasuwan ya kara da cewa kamfanin NNPCL yana iya bakin kokarinsa wurin zakulo hanyar dakile matsalar tare da buɗe wasu ma'ajiyar man.

"Gwamnatin Najeriya ce ke shigo da mai din kasar, idan suka shigo da shi sai su ba ga dillalan mai domin rarraba shi."
"Abin da muke da shi, shi za mu bayar, ba za mu ba da abin da bamu da shi ba."

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Hazikin dalibi dan shekara 18 ya samu maki 313 a jarabawar UTME

"Amma gwamnati ta na iya bakin kokari, domin a ranar Litinin ma kamfanoni NNPCL ya ce zai buɗe wasu ma'ajiyoyin man domin samun shi cikin sauki."

- James Tor

James Tor ya ce shugban IPMAN ya kira shi kan karin shigo da man da aka samu a Najeriya.

"Kun ga wannan matsalar a Gabas ta Tsakiya na rikicin Iran da Isra'ila ya na matukar kawo cikas ga samar da man a Najeriya."

- James Tor

IPMAN ta yi alkawari kan matsalar mai

Kun ji cewa kungiyar dillalan mai a Najeriya, IPMAN ta yi karin haske kan wahalar mai da ake fama da shi a kasar.

Kungiyar ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa nan da makwanni biyu komai zai wuce ya zama tarihi kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.