Ana Murna Yayin da Naira Ta Sake Farfaɗowa, Ta Yunƙuro da 1.98% a Kasuwa

Ana Murna Yayin da Naira Ta Sake Farfaɗowa, Ta Yunƙuro da 1.98% a Kasuwa

  • Yayin da naira ke sauka ta tashi a 'yan kwanakin nan, darajarta ta sake mikewa a kasuwanni a ranar Talata 30 ga watan Afrilu
  • A kasuwanni ana siyar da ita kan N1,390 wanda hakan ke nuna ta tashi idan aka kwatanta da ranar Litinin 29 ga watan Afrilu
  • Tashin darajar naira a ranar Talata 30 ga watan Afrilu ya nuna karin 1.98% kenan idan aka kwatanta da ranar Litinin 29 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Bayan samun matsaloli a 'yan kwanakin nan, darajar naira ta tashi a jiya Talata 30 ga watan Afrilu.

Naira ta samu ƙaruwa da kusan N28.15 yayin da ake siyar da ita N1,390.96 kan kowace dala a kasuwanni.

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Hazikin dalibi dan shekara 18 ya samu maki 313 a jarabawar UTME

Darajar naira ta sake farfadowa a kasuwar 'yan chanji
Bayan samun matsala a ranar Litinin, naira ta sake ƴunkurowa a kasuwar 'yan chanji. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Yadda Naira ta sake tashi a kasuwa

Bayanai daga hukumar kula da cinikayyar kudin, FMDQ ta tabbatar da cewa karin da aka samu a darajar naira ya kai 1.98%, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin kason da aka samu ya na da muhimmanci idan aka kwatanta da cinikayyar da aka yi a ranar Litinin 29 ga watan Afrilu.

Makwanni biyu da suka gabata Naira ta sha bugu a hannun dala inda ake siyar da ita kan kudi N1,419 a kasuwanni, cewar Vanguard.

Musabbabin tashin darajar Naira a kasuwa

Sai dai a bangaren masu zuba hannun jari da masu fitar da ita, ana cinikin dala kan N1,200 zuwa N1,450.

Wannan tashin darajar Naira bai rasa nasaba da yawan kudi da ake cinikayya wanda kullum ya ke karuwa a kasuwanni.

An samu karin yawan kasancewar dala da ya kai $255m a ranar Talata idan aka kwatanta da $157m a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPCL ya dauki matakin kawo karshen dogon layin da ke gidajen mai

Darajar Naira ta sake tashi a kasuwa

A wani labarin, kun ji cewa kudin Najeriya watau Naira ya kara kima a kasuwannin canji da na bayan fage bayan an tabbatar dalar Amurka ta tashi.

Bayanan da aka samu ya nuna Naira ta tashi domin kuwa an saida ta a kan kimanin N1,200 a kasuwa a cikin karshen makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.