1 Ga Watan Mayu: Gwamnati Ta Fadi Ranar da Sabon Albashin Ma’aikata Zai Fara Aiki

1 Ga Watan Mayu: Gwamnati Ta Fadi Ranar da Sabon Albashin Ma’aikata Zai Fara Aiki

  • Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce sabon mafi karancin albashin ma’aikata zai fara aiki a ranar 1 ga Mayu, 2024
  • Onyejeocha yi nuni da cewa gwamnati za ta aiwatar da karin duk da cewa kwamitin karin albashin bai kammala aikin da aka bashi ba
  • A hannu daya kuma, Shugaba Bola Tinubu ya yaba da gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a Najeriya wajen ci gaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce sabon mafi karancin albashin ma’aikata a Najeriya zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Mayu, 2024.

Gwamnatin ta ce ta yanke wannan hukuncin duk da cewa kwamitin da ke da alhakin ba da shawa kan karin albashin ma'aikata bai gabatar da rahotan tattaunawarsa ba.

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

Gwamnati ta fadi ranar da sabon albashin ma'aikata zai fara aiki
Gwamnati ta ce sabon albashin ma'aikata zai fara aiki ranar 1 ga watan Mayu, 2024. Hoto: @nkeiruka_reps
Asali: Twitter

Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bayyana hakan a ranar laraba yayin da take jawabi ga ma’aikatan Najeriya, a cewar rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce gwamnati ba ta ji dadin yadda sabon mafi karancin albashin na kasa bai fara aiki kafin yau ba, amma ta ce komai zai kammala nan ba da jumawa ba.

Matsayar NLC da TUC kan sabon albashi

Kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC a lokuta daban-daban sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta sake duba batun albashin ma’aikata.

A baya-bayan nan ne kungiyar kwadago ta nemi N615,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata domin shawo kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Kungiyoyin kwadagon sun ce mafi karancin albashi na N30,000 a halin yanzu ba zai iya samar da walwala ga kananan ma'aikata a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwamiti ya dauki mataki kan zargin badakala, ya fadi tsare tsaren Bincike

Tinubu ya jinjinawa ma'aikatan Najeriya

A hannu daya kuma, gidan talibin na TV360 ya ruwaito Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a Najeriya wajen ci gaban kasar.

Tinubu yi wannan yabon ne a jawabinsa ga ma’aikatan ta bakin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a wajen taron bikin ranar ma’aikata ta 2024 a Abuja.

Ya ce kofar gwamnatin tarayya a bude take domin karbar shawarwarin kwamitin da aka kafa kan sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Ranar ma'aikata: Gwamnati ta ba da hutu

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu a Najeriya domin bikin murnar ranar ma'aikata.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu a madadin gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel