Mata Mai Ciki ta Tsallake Rijiya da Baya a Wata Muguwar Gobara a Legas
- Wata mai juna biyu da wasu mutum 18 sun tsallake rijiya da baya bayan tashin gobara a Legas, inda su ka ji munanan raunuka
- Gobarar ta tashi ne bayan tukunyar gas ta fara yoyo, inda ta taba babbar wayar wuta a yankin, amma ba a samu rahoton rasa rai ba
- An tafka asarar ababen hawa da shaguna da bangaren wani gidaje, amma hukumar kashe gobarar ta ce ta yi kokarin shawo kan wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Lagos - Wata mai juna biyu ta tsallake mutuwa bayan yoyon da tukunyar gas ta yi ya haddasa mummunan gobara a yankin Ajegunle-Apapa da ke jihar Legas.
Wasu mutane 18 da wannan mata mai juna biyun sun samu munanan raunuka a gobarar da ta afku jiya a yankin.
Jami'an Legas sun kashe gobarar
A cewar hukumar kashe gobarar jihar ta shafinta na X, cikin mutane 19 da su ka ji raunuka har da kananan yara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da munin gobarar, ba a samu rahoton asarar rai a wurin gobarar ba.
Amma an tafka asara a gobarar
A cewar Margaret Adeseye, shugabar hukumar kashe gobarar da bayar da agaji ta jihar Legas an tafka asara kai yawa a gobarar.
Shugabar ta ce daga abubuwan da aka rasa akwai babura masu kafa uku guda hudu, shaguna shida, da wani bangare da wani gida da ke kusa da wajen gobarar.
Amma ta bayyana kokarin jami'an hukumar na hana wutar yaduwa zuwa wani gidan mai a yankin, kamar yadda Channels Television ta wallafa.
Margaret Adeseye ta ce kokarin ma'aikatan ya taimaka sosai wajen dakile yaduwar wutar.
Wadanda su ka ji raunuka yanzu haka na babban asibitin Ajeromi da ns Gbagada Burnt & Trauma Centre su na karbar magani.
Wata kasuwa ta kone a gobara
Mun ruwaito mu ku a baya cewa wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar Owode dake Offa a jihar Kwara tare da janyo dumbin asara.
Yan kasuwa na tsaye su na kallon wutar ta na cinye shagunansu, amma su ka gagara kashe ta, har gobarar ta lakume dukiyoyin miliyoyin Naira.
Asali: Legit.ng