Tinubu Ya Amince da Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi, Bayanai Sun Fito

Tinubu Ya Amince da Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sanar da yi wa ma'aikata ƙarin albashi
  • Ma'aikatan da ke kan tsarin albashi na bai ɗaya za su samu ƙarin albashi da kaso 25% zuwa kaso 30% a kan wanda suke karɓa a yanzu
  • Sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa ya sanar da hakan inda ya ƙara da cewa ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar, 1 ga watan Janairun 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da yin ƙarin albashi ga ma’aikatanta da kaso 25% zuwa kaso 35%.

Ma’aikatan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa ƙarin albashi sun haɗa da masu karɓar albashi na bai-ɗaya na CONPSS, CONRAISS, CONPOSS, CONPASS, CONICCS da CONAFSS.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta bayyana matsayarta kan karin albashin da gwamnatin Tinubu ta yi

Tinubu ya yi karin albashi ga ma'aikata
Gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikata karin albashi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tashar NTA a shafinta na X ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa, Emmanuel Njoku, ya fitar a ranar Talata, 30 ga watan Janairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika gwamnatin tarayya ta yi ƙarin albashi ga ƴan fansho da kaso 20% zuwa kaso 28% a kan albashinsu na yanzu.

Yaushe ƙarin albashin zai fara aiki?

Emmanuel Njoku ya bayyana cewa ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar, 1 ga watan Janairun 2024.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin tarayya ta yi ƙarin albashi ga ma'aikatan makarantun gaba da sakandare da ɓangaren lafiya.

Wannan ƙarin albashin dai na zuwa ne ana a yayin da ake shirin bikin ranar ma'aikata ta duniya a ranar Laraba, 1 ga watan Mayun 2024.

Gwamnatin tarayya ta sha samun kiraye-kiraye daga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a kan ta yi wa ma'aikata ƙarin albashi saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita, sakamakon cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kwara ya halarci kotu yayin da EFCC ta gurfanar da kwamishina kan N1.22bn

An ƙara mafi ƙarancin albashi a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan.

Gwamna Obaseki ya sanar da haka ne yayin ƙaddamar da sabon ofishin ƴan kwadago na jihar, inda ya ce sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne daga ranar, 1 ga watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng