Yan Bindiga Sun Sake Kai Kai Hari Abuja, Sun Yi Garkuwa da Mutum 4 Har da Fasto
- A daren ranar Talata ne 'yan bindiga suka kai wani hari kan al'ummar garin Bmuko a Dutse Baupma, da ke babban birnin tarayya Abuja
- Wani mazaunin unguwar, Mista Isah, ya ce an kai farmakin ne da misalin karfe 11:50 na dare kuma sun sace Fasto da wasu mutum uku
- Wannan dai shi ne hari na biyu da 'yan bindigar suka kai wa al'umar Dutse a kasa da mako daya, inda suka sace mutum biyar a harin farko
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bwari, Abuja - 'Yan bindiga sun kai farmaki kan al’ummar Bmuko a Dutse Baupma, karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
A yayin harin da suka kai ranar Litinin da daddare, an ruwaito cewa sun samu nasarar yin garkuwa da mutane hudu a garin.
Yadda 'yan bindiga suka kai hari Abuja
Wani mazaunin unguwar, Mista Isah, ya ce an kai farmakin ne da misalin karfe 11:50 na dare a gidan wani Injiniya Patrick, wanda aka tafi da matarsa da dan uwansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, 'yan bindigar da yawansu ya kai 30, sun afkawa anguwar shiyya ta C, titi na 5 a garin inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, jaridar Leadership ta ruwaito hakan.
“Daga gidan Injiniya, bayan dauke da matarsa da dan uwansa, sai suka rabu gida biyu. Wasu suka nufi anguwannin yankin Kubwa da Bwari, yayin da wasu suka nufi wani yankin.
“Tawagar da ta nufi anguwannin da ke kusa da tsauni ne suka tsaya a wani gida inda suka yi garkuwa da wani Fasto da wani matashi."
- A cewar Mista Isah.
'Yan bindiga sun sace mutum 5
Wannan na zuwa kasa da mako daya da 'yan bindigar suka kai makamancin wannan harin a yankin Dutse da ke karamar hukumar Bwari.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, inda kuma suka yi garkuwa da mutum biyar.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce al'ummar da ke zaune a yankin ba su iya yin barci a wannan daren ba saboda fargaba.
An kama dillalin wiwi a Kano
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani rikakken dillalin miyagun kwayoyi da ta dade tana nema ruwa a jallo.
Dillalin kwayoyin da ake kira da Badoo ya yi kaurin suna a yankin Tukuntawa da fadin jihar inda yake raba kwayoyi ga matasa da matan aure.
Asali: Legit.ng