Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Kafa Dokar Wajabta Gwajin Lafiya Kafin Aure
- Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kirkiro dokar fara tantance lafiyar ma'aurata kafin aure a zamanta na jiya Litinin
- 'Yan majalisar sun kirkiro dokar ne domin kare al'umma daga kamuwa da cututtukan da ke zama barazana ga lafiya ta hanyar auratayya
- A halin yanzu ana jiran Mai girma gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sa hannu kafin dokar ta fara aiki a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da kafa dokar gwajin lafiya tsakanin ma'aurata kafin aure.
Sabuwar dokar za ta tilastawa duk wanda za su yi aure gwajin lafiya domin kaucewa yaɗuwar cututtuka da za su zama barazana ga al'umma.
Wadanne cututtuka za a rika gwaji a Kano?
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa an sanya gwajin cutar kanjamau, ciwon hanta da sikila a matsayin gwaje-gwajen da suka zama wajibi kafin aure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta zartar da dokar ne a jiya Litinin yayin zaman da ta gabatar, cewar jaridar Daily Nigerian.
Dalilin kafa dokar gwaji a jihar Kano
Shugaban majalisar, Ismail Falgore ya ce dokar ta zama wajibi a wannan lokaci inda aka samu yawaitar cututtuka masu barazana ga lafiyar al'umma da dama.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin, Lawan Hussein, ya ce an samu yawaitar yaɗuwar cututtuka ta hanyar aurataya kuma saboda dakile matsalar ne suka kirkiro dokar.
Yaushe dokar za ta fara aiki a Kano?
Yanzu dai za a saurari gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, domin saka hannun kan dokar kafin ta fara aiki a fadin jihar.
Ana sa rai idan aka saka hannu kan dokar za ta kawo sauki a kan matsalar rashin lafiya da ake fiskanta bayan aure a jihar.
Kwamitin binciken Ganduje ya fara aiki
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin binciken tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kan rashawa ya fara aiki.
A zaman kwamitin na jiya Litinin, ya bada sanarwa ga al'ummar jihar da su taimaka da bayanai na musamman domin sanin hakikanin gaskiya lamarin.
Shugaban kwamitin ya ce a shirye suke su tabbatar da cewa an yiwa ko wanne bangare adalci cikin binciken.
Asali: Legit.ng