'Idan dai Babu Wuta, Babu Biyan Sabon Kudin Lantarki', Minista ya zuga 'yan Najeriya
- Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya shawarci yan Najeriya kan matakin da za su dauka a kan rashin wuta
- Ministan ya ce ka da wanda ya biya sabon kudin wutar da bai sha ba yayin da ake fama da karancin wutar a fadin Najeriya
- Adebayo Adelabu ya bayar da shawarar ne lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya umarci yan Najeriya da ka da su kuskura su biya kudin wutar da ba su sha ba.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke fama da matsanancin rashin wutar lantarki bayan an canza farashi.
Ministan ya jaddada cewa duk kwastomomin da ke kan layin band A da B da aka yi wa alkawarin samun wutar awa 20, kuma ba sa samu, su rike kudinsu, kamar yadda Leadership News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai kamata yan Najeriya su biya sabon kudin wutar lantarki ba idan ba sa samun wuta.
Gwamnati za ta biya tallafin wutar lantarki
Ministan wutar lantarkin,wanda ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki a Litinin dinnan ya ce gwamnati za ta biya tallafin wutar lantarki.
Ya kara da cewa ana bukatar akalla Dala biliyan 10 duk shekara na tsawon shekaru 10 kafin a iya farfado da sashen wutar lantarki a Najeriya, kamar yadda Punch News ta ruwaito.
Ministan na ganin wannan ba zai yiwu ba ganin girman kasafin da sashen ke bukata.
A bangaren tallafi kuma Minista Adebayo Adelabu ya ce idan ba a duba farashin wutar ba, gwamnatin za ta biya Naira Tiriliyan 2.9 na tallafi ga bangaren.
Ya ce gwamnati ta bijiro da sababbin matakan ceto bangaren wutar lantarki a kasar nan, har ma ya ce wahalar da ake sha yanzu ba za ta dore ba.
Gwamnati za ta yi gwanjon DISCOs
A baya kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce za ta sayar da wasu kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki (DISCOS) guda biyar a kasar nan.
Wannan alwashi na zuwa ne a sa'ilin da hasken wutar ya yi karanci, kuma ake ci gaba da bukatar wutar saboda tsananin zafi.
Asali: Legit.ng