Jiragen Ruwa 3 Jibge Da Man Fetur Lita 98.8m Sun Dira Tashar Jirgin Legas

Jiragen Ruwa 3 Jibge Da Man Fetur Lita 98.8m Sun Dira Tashar Jirgin Legas

  • Sama da watanni shida kenan yan Najeriya na fama da tsadar man fetur da yaki ci, yaki cinyewa
  • Bayan watannin gwamnati ta kara farashin man fetur inda Gidajen man kamfanin NNPCL suka koma sayar da Lita N190
  • A mafi akasarin jihohin Arewa, an dade ana sayar da litan man fetur har sama da N300

Legas - Jiragen ruwa dauke da litan man fetur milyan 98.9 sun dira a tashar jirgin ruwan Legas karshen makon nan, bayanai daga hukumar tashoshin jirgin ruwa NPA suka nuna.

Bayanan sun nuna cewa jirgin ruwan da aka yiwa lakabi da Antares1 ya dira tashar ruwan Legas ranar Juma'a da ton 36,000 na man fetur, rahoton Vanguard.

Jirgin Ocean Nirvana ya dira da ton 36,932 na mai ranar Juma'ar dai, sannan kuma jirgin Zonda ya dira da ton 25,882 na man fetur ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Bukaci NDLEA Ta Kama Bola Tinubu, Ya Bayyana Dalilai

Hakazalika ana sauraron ton 4,758 na man fetur ya isa Legas ranar Litinin, 23 ga Junairu, 2023.

Vessel
Jiragen Ruwa 3 Jibge Da Man Fetur Lita 98.8m Sun Dira Tashar Jirgin Legas
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da kari ana kyautata zato jirgin M/T Montago ya isa da ton 25,000 na Man Gas (AGO) da ton 5000 na man jirgin sama (JET A1) ranar Juma'ar.

Yayinda jirgin M/T Berners ya dira da ton 14,500 na JET A1 da AGO ranar Asabar.

Ko yau Lahadi, bayanan hukumar NPA sun nuna cewa jiragen ruwa biyu; M/T Alfred Temile da M/T Sapet zasu dira dauke da iskar Gas ton 12,000.

Gwamnatin Buhari Ta Gaji da Dogayen Layin Mai, Ta Kara Farashin Man Fetur

Bayan wata da watanni yan Najeriya na fama da wahala da tsadar man fetur, gwamnatin tarayya ta amince da karin naira 15 a kan farashin litar man fetur,

Kara karanta wannan

Gwamnati ta Sanar da Sabon Farashin Litar Fetur, An Amince da Karin 8.8% a Najeriya

Farashin litan mai ya tashi tanzy daga N180 zuwa N195.

Kawo ranar Juma’a, 20 ga watan Junairu 2023, ta ce mafi yawan gidajen mai su na saida fetur ne a farashin da ya zarce haka, rahoton Vanguard.

Da alamu Gidajen man da ke karkashin kungiyar ‘yan kasuwa na MOMAN sun bi wannan umarni, kuma sun canza farashin litar su kamar yadd aka yi umarni.

A birnin tarayya Abuja, tuni farashin ya sauya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel