Tinubu Ya Fara Shirin Yin Waje da Wasu Ministocinsa Kafin Cika Shekara 1 a Mulki
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kusa cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya bayan ya kama rantsuwar aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023
- Alamu sun nuna kafin shugaban ƙasar ya cika shekara ɗaya a mulki, zai yi waje da wasu daga cikin mambobin majalisar ministocin tarayya
- Tun da farko shugaban ƙasan ya nuna cewa zai tafi ne kawai da waɗanda za su iya yin aikin da ke gabansu yayin da zai sallami waɗanda suka nuna gazawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara shirye-shiryen gudanar da bikin cika shekara ɗaya a kan karagar mulkin Najeriya.
Shugaban ƙasar ya yi rantsuwar kama aiki ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023, bayan ya karɓi mulki a hannun tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Jaridar The Guardian ta kawo rahoto cewa alamu sun nuna cewa shugaban ƙasar zai yi wa majalisar ministocinsa garambawul.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne ministoci za a kora?
Rahotanni sun nuna cewa wasu ministocin za a yi waje da su a maye gurbinsu kafin nan da ranar, 29 ga watan Mayu, yayin da za a yi wa wasu sauyin ma'aikatu.
Shugaba Tinubu zai kuma yi amfani da lokacin domin duba naɗin da ya yi wa wasu daga cikin ministocinsa masu matsala da hukumar EFCC.
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Shugaba Tinubu a yayin wani taron bita ya yi nuni da cewa za a riƙa auna ministocin a sikeli lokaci bayan lokaci domin ganin ayyukan da suke yi.
Ya kuma sha alwashin korar duk waɗanda ba su taɓuka abin arziƙi a cikin majalisar ministocin nasa, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Daga nan shugaban ƙasan ya samar da wata tawaga wacce za ta riƙa duba ayyukan ministocin, hukumomi da ma'aikatun tarayya.
Tinubu ya nemi haɗin kai
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi haɗin kan duniya wajen yi wa matsalar yunwa taron dangi domin kawar da ita.
Shugaban ƙasan ya nemi hakan ne a taron duniya kan tattalin arziki da makamashi da ya gudana a birnin Riyadh na Saudiya.
Asali: Legit.ng