Kamfanin Denmark Zai Zuba $600M a Harkar Sufurin Jirgin Ruwa Na Najeriya

Kamfanin Denmark Zai Zuba $600M a Harkar Sufurin Jirgin Ruwa Na Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da shugaban kungiyar A.P Moller-Maersk, Robert Uggla, a taron tattalin arzikin duniya a Saudiya
  • A yayin ganawar, kamfanin AP Moller-Maersk ya yi alkawarin zuba jarin $600M domin bunkasa tashar jiragen ruwan Najeriya
  • A cewar Tinubu, za a yi amfani da kudaden wajen fadada gine-ginen tashoshin jiragen domin kara yawan jigilar kwantena a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudi - Najeriya ta samu jarin $600m daga AP Moller-Maersk, wani kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark, domin bunkasa gine-ginen tashar jiragen ruwan kasar.

Najeriya da kamfanin Denmark sun shiga yarjejeniyar $600m
Kamfanin Denmark zai zuba jarin $600m a Najeriya, za a bunkasa tashoshin jiragen ruwa. Hoto: @DOlusegun, @Maersk
Asali: Twitter

Yadda jarin Maersk zai amfani Najeriya

Robert Uggla, shugaban kungiyar A.P Moller-Maersk, ya yi alkawarin zuba jarin ne a wata ganawa da Bola Tinubu a taron tattalin arzikin duniya (WEF) a kasar Saudiyya ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Ondo: An kashe kodinetan yaƙin neman zaben gwamnan APC, 'yan sanda sun magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce ya nemo jarin ne domin fadada gine-ginen tashar jiragen ruwa da ake da su a Najeriya domin fadada ayyukan jigilar kwantena a tashoshin, rahoton The Cable.

Ya ce wannan yarjejeniyar za ta taimaka wajen cimma kudirin gwamnatinsa na zuba jarin dala biliyan daya, a farfado da tashar jiragen ruwa a sassan gabashi da yammacin Najeriya.

"Akwai lada a zuba jari a Najeriya" - Tinubu

Tinubu ya ce kudaden za su kara tallafawa kokarin sabunta tashar jiragen ruwa na Najeriya da sarrafa tashoshin a tsari na zamani domin gogayya da kasashen ketare.

Tinubu ya shaidawa Uggla cewa:

“Mun yaba da tsarin kasuwancin ku da gudummawar da kuka bayar kuma kuke ci gaba da ba bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasarmu,
“Duk wanda ya zuba jari a Najeriya ba zai yi da-na-sani ba. Hakanan zuba jari a kasar mu zai samar da gwaggwabar lada fiye da wadda za a samu a wani wuri."

Kara karanta wannan

2027: Matasan Arewa sun gano shirin kawo cikas ga Tinubu da 'yan siyasa ke ƙullawa

Karin damarmakin zuba jari a Najeriya

A rahoton Vanguard, shugaban ya bayyana cewa akwai karin damar saka hannun jari a Najeriya, kuma gwamnatinsa ta yi kokarin yin gyare-gyare domin karfafa zuba jarin.

Tinubu ya tabbatar wa Uggla kudirin gwamnatin sa na hada kai da masu zuba jari domin samar da yanayin da zai sa ‘yan kasuwa su bunkasa a Najeriya.

Ya ba da misali da haɗin gwiwar da Maersk ta yi a baya wajen haɓaka tashar kwantena ta jihar Ogun a matsayin shaida na haɗin gwiwa da ta samar da riba.

Dubai za ta gina tashar jirgin sama

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kasar Dubai da ke a hadaddiyar daular Larabawa (UAE) za ta gina tashar jirgin sama mafi girma a duniya.

Za a kashe akalla Naira tiriliyan 43 a wajen gina wannan tashar wadda ake sa ran kammala kashin farko nan da shekara 10, tare da fara jigilar akalla fasinjoji miliyan 150.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.