Irin amfanin da tashar jirgin ruwan kan tudu za tayi wa Arewacin Najeriya
- Shugaban Kasa Buhari ya bude wani tashan ruwa jiya a Kaduna
- Wannan ne tashar jirgin ruwa ta farko a kaf Arewacin Najeriya
- Masu safarar kaya a Yankin sun samu sauki har cikin gida yanzu
Idan ku na biye da mu za ku san cewa a jiya Alhamis ne Shugaba Buhari ya bude wani katafaren tashan jirgin ruwa na kan tudu a Garin Kaduna. Wannan ne irin sa na farko a Yankin. Yanzu haka sufurin kaya ya zo har Arewa inda babu ruwa.
Wannan tasha za ta taimakawa masu shigowa ko ficewa da kaya daga Yankin har zuwa wajen kasar. Budu da kari dai ana za a rika yin duk takardun da ake bukata na shiga ko fita da kaya cikin Najeriya kamar yadda mu ka fahimta.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bude tashar kan tudu na farko a Arewa
Za a sa hannu a nan domin daukar kayan da su ka shigo ta tashar da ke kan tudu, sannan kuma za a iya aika kaya zuwa ketare kamar yadda ake yi a tashar gaban teku. Tashar na hade ne kuma da hanyar jirgin kasa na Legas zuwa Kano.
Tashar dai za ta taimakawa mutanen da ke Arewacin Najeriya da ke fama da wahala iri-iri wajen fita ko shiga da kaya ketare wanda sai sun tafi har Kudancin Kasar domin su samu kai ga tashar gaban teku.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng