Zarqa Al Yamama: Saudiya Ta Fara Gabatar da Wasan Daɓe da Raye-Raye Na Farko a Tarihi
- Kasar Saudiya ta bude gidan wasan daɓe da raye na farko a birnin Riyadh kuma har an fara gabatar da wasan farko
- 'Zarqa Al Yamama' shine wasa na farko da aka fara gabatarwa, wanda za a kammala gabatar da shi a ranar Asabar 4 ga Mayu
- Ivan Vukcevic, wanda ke shugabantar gidan wasan ya ce an fuskanci matsaloli a lokacin da ake shirye-shiryen gabatar da wasan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Riyadh, Saudiya - A kokarinta na ganin ta shiga sahun kasashen duniya domin ayi gogayya da ita a fannin nishadi, Saudiya ta bude gidan wasan daɓe na farko a birnin Riyadh.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, an gabatar da wasan farko na daɓe da raye-raye a gidan wasan wanda ya samu halartar mutane da dama.
Wasan farko da aka fara gabatarwa
Da alama dai, Yarima Mohammed bin Salman ya toshe kunnuwa daga cece-kucen jama'a kan tsare-tsaren da yake kawowa na mayar da masarautar ta daban ta fuskar nishadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Zarqa Al Yamama' shine wasa na farko da aka fara gabatarwa, wanda yake bayar da labari shugabar wata kabilar mutane masu koren idanu.
An ce tarihin al'umar ya zo ne tun gabanin addinin Musulunci ya shiga cikin ƙasashen labarabawa.
Ivan Vukcevic, wanda ke shugabantar gidan wasan na Saudiya ya ce labarin sarauniyar da yadda al'umarta suka ƙaryata hasashen annobar da ke tunkararsu zai ja hankalin duniya.
Shirin bude gidan wasa a Saudiya
Zarqa Al Yamama na dauke da wasanni goma, wanda za a kammala gabatar da su a ranar Asabar 4 ga Mayu 2024, in ji jaridar PRNewswire.
A shekarun baya, wani kamfanin kasar Switzerland ne aka samu ya dauki nauyin koyar da wasan na farko da kuma koyar da rawa da kiɗe-kiɗe.
Mista Vukcevic ya ce ya fada cikin tsananin mamaki a lokacin da aka ce za a bude gidan wasa a kasar Saudiya kuma har ana gayyatarsa da ya jagoranci gidan.
Matsalolin da aka fuskanta kafin wasan
A tunaninsa, irin hakan ba za ta taɓa faruwa ba, inda har ya yi shakku kan faruwar hakan saboda tunanin za a fuskanci kalubale daga masu suka.
Daga cikin matsalolin da aka fuskanta a shirye-shiryen gudanar da wasan na farko akwai matsalar buga kidan wasan.
Kasancewar ana yin rubutun Larabci daga dama zuwa hagu, yayin da su kuma makidan na amfani da Ingilishi daga hagu zuwa dama, hakan ya kawo tsaiko.
Sai dai an ce an shawo kan wannan matsalar bayan dogon lokaci ana nazari da bincike da kuma koyar da kidan a kasashen yamma a tsarin rubutun Larabci.
An bude shagunan barasa a Saudiya
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, kasar Saudiya ta bude shagunan sayar da barasa a birnin Riyadh bayan shekara kusan 70 da haramta sayar da giya a kasar.
Sai dai kasar ta ce an bude shagunan ne saboda jami'an jakadancin kasashen ketare da ke kawo ziyara kasar ba wai domin 'yan kasar su siya ba.
Asali: Legit.ng