Juyin Zamani: Rawar mata a kasar Saudiyya a kulob ta fara tayar wa da kasar hankali

Juyin Zamani: Rawar mata a kasar Saudiyya a kulob ta fara tayar wa da kasar hankali

- Bidiyon ya nuna mata, kusan dukkaninsu fuskar su rufe da niqab, suna rawa ga wakar da wani mawaki ke rerawa a wani gurin shakatawa a arewacin birnin Arar

- Ma'abota amfani da tweeter na kasar sun bayyana damuwar su na rawan da mata sukeyi wanda zai yuwu maza na kallon su

Juyin Zamani: Rawar mata a kasar Saudiyya a kulob ta fara tayar wa da kasar hankali

Juyin Zamani: Rawar mata a kasar Saudiyya a kulob ta fara tayar wa da kasar hankali

Video din mata suna rawa a wani gidan rawa Saudi Arabia ya fusata filayen sada zumunta na, wadanda suke ikirarin hakan ya sabawa tarbiyar daular musuluncin.

Bidiyon ya nuna mata, kusan dukkaninsu fuskar su rufe da niqab, suna rawa ga wakar da wani mawaki ke rerawa a wani gurin shakatawa a arewacin birnin Arar.

Ma'abota amfani da tweeter na kasar sun bayyana damuwar su na rawan da mata sukeyi wanda zai yuwu maza na kallon su.

"Idan mata suka zama fitsararru, toh tabbas kasar nan na cikin masifa, " inji ma'abota tweeter.

Wasu kuma suka ce "Wannan abin bakin ciki ne, yakamata a tuhumi gurin shakatawar"

Gurin shakatawar yayi gobara sakamakon zargin da ake musu da hada mata da maza, wanda ya haramta a Saudi Arabia.

A bidiyon, an nuna katanga tsakanin matan da mazan, amma katangar bata rufe tsakanin su ba har zuwa kan mumbarin.

A gaba an nuna mata da maza na rawa suna fuskantar juna.

Bayan yaduwar bidiyon, Daraktan gurin shakatawar yace sunyi kokarin hana matan yin rawa ta hanyar basu umarnin komawa mazaunin su, tare da dakatar da mawakin.

DUBA WANNAN: Maradona ya yo kashedi kan wasansu da Najeriya

Ya kuma ce katangar ta raba matan da mazan, an dai dau bidiyon ne ta inda ake hange kamar katangar bata kai gurin mumbarin ba.

A watan fabrairu na shekarar nan ne, aka kama wasu ma'aurata sakamakon rawa da aka gansu suna yi akan titi.

A shekarar da ta gabata ne, yan sandan suka kama yaro Dan shekaru 14, saboda yana rawa akan Macarena a birnin Jeddah. Sun kira hakan da rashin tarbiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel