Batun bude gidan rawa a Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a

Batun bude gidan rawa a Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a

Lamarin bude wani gidan rawa na halal a birnin Jiddah da ke kasar Saudiyya ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta na kasar, inda mutane ke tofa albarkacin bakunansu.

Wani gidan rawa na birnbin Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna White ne ya sanar da bude sabon gidan rawar da ya kira "Halal Disco" a Jiddah a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Kafofin yada labarai na kasar sun tabbatar da bude gidan rawar wanda suka ce tsarinsa ya yi matukar kama da gidan casu na dare da aka sani, sai dai kuma ba za a dinga shan barasa a wajen ba.

Shi ma gidan rawar na White ya ce wurin zai yi kama ne da dakin hira ba da mashaya ba.

Wasu rahotannin sun kuma ce mata ba za su sanya abaya ba, amma mamallakan wajen sun ce yanayin suturar da za a dinga sa wa za ta zama sassauka.

Wannan batu dai ya raba kan 'yan kasar biyu inda wasu suka tunzura da labarin tare da yin Allah-wadai da matakin gwamnati na ba da damar bude gidan rawar a kasar, wacce suke ganin tana kare kimarta tsawon gomman shekaru.

KU KARANTA KUMA: Bamu da wata na’ura – INEC ta mayar da martani ga Atiku

Amma a daya bangaren wasu murna suke da samun gidan rawar, irinsa na farko a kasar.

Masu sukar lamarin dai suna ta kira ga hukumomin kasar da kar su bari a bude gidan rawar na dare, suna masu cewa ya kamata a kare tare da tsare kyawawan al'adu na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel