Jerin sauye-sauye 8 da Yariman Saudiyya ya kawo kasar ta fannin nishadi

Jerin sauye-sauye 8 da Yariman Saudiyya ya kawo kasar ta fannin nishadi

Har yanzu dai batun zuwan mawakiya Niki Minaj kasar Saudiyya don yin waka na ci gaba da kawo kace-nace a shafukan sadarwa.

Nicki Minaj dai za ta je kasar ne a ranar 18 ga watan Yuli a wajen taron raye-raye na shekara-shekara wato Jeddah World Fest.

Duk da cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan sauyin ba, ana nuna damuwa kan zuwan Minaj ne musamman ganin irin shigar da mawakiyar ke yi a lokacin da take waka, a kuma kasar da ake yi wa kallon 'mai tsaurin ra'ayi'.

Ana ganin cewa Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado ne ke kawo wadannan sauye-sauye a kasar musamman a bangaren nishadantarwa.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Adeleke yayi martani, yayi wa Oyetola fatan alkhairi

Ga wasu daga cikin sauye-sayen da ya kawo a kasar mai tsarki:

1. Dage haramci kan sinima

A watan Disambar 2018 ne, gwamnatin Saudiya ta dage haramci kan gidajen sinima.

Tuni dai Saudiyyar ta sanar da bayar da damar bude gidajen nuna fina-finai a kasar.

2. Dage haramcin tuki ga mata

A watan Satumbar 2018 ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da dage haramcin tuki ga mata, kuma tuni aka fara bai wa matan lasisin tuki a Saudiyya.

Kafin dage haramcin Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin yin tuki.

3. Bude gidan rawa a Saudiyya

A watan Yunin 2019 wani gidan rawa na birnbin Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna White ya sanar da bude sabon gidan rawar da ya kira "Halal Disco" a Jiddah.

4. Bikin kafa Saudiyya da ya kawo gwamutsa mata da maza

A karon farko an ba mata damar shiga wani filin wasanni don bikin zagayowar ranar 'yancin kan Masarautar Saudiyya.

A watan Satumbar 2017 ne filin wasa na Sarki Fahad a Riyadh babban birnin ƙasar, ya maƙare da ɗaruruwan matan da suka yi ɗango don cin wannan gajiya.

5. Tarukan casu

Tawagar mawaka ta Cirque Éloize ce ta farko da suka yi casu a watan Janairun 2018 wanda shi ne karon farko a birnin Dammam na Saudiyya.

6. Shigar mata wajen kallon kwallo

7. Kallon 'yan kokawa na Amurka

A karon farko a watan Afrilun 2018 an bai wa mata da maza damar shiga kallon wasan kokawa na Turawan Amurka.

An gudanar da damben kokawar na (WWE) a birnin Jiddah, kuma maza da mata ne suka shiga kallo wanda kafar telebijin din kasar ta nuna kai tsaye.

8. Tseren keken mata zalla

A watan Afrilun 2018 ne kuma aka gudanar da tseren keken mata na farko a kasar Saudiyya, inda suka bai wa mutane da yawa mamaki a kasar ta masu ra'ayin mazan-jiya, musamman a shafukan sada zumunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel