Naira Tayi Zuciya, Darajar Kudin Najeriya Ta Farfado a Kasuwar Canji

Naira Tayi Zuciya, Darajar Kudin Najeriya Ta Farfado a Kasuwar Canji

  • Naira ta sake yunkurin tashi a kasuwannin bayan fage da hannun manyan bankuna a cikin karshen makon nan
  • Gwamnan CBN ya kashe $15m wajen rabawa masu canji $10, 000 da nufin magance karancin kudin kasashen ketare
  • Bayanan da ke kafar FMDQ ya nuna farashin Naira bai tashi ba duk da an samu rangwame a kasunnin bayan fage (BDC)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kudin Najeriya watau Naira ya kara kima a kasuwannin canji da na bayan fage bayan an ji cewa Dalar Amurka ta tashi.

Bayanan da aka samu ya nuna Naira ta tashi domin kuwa an saida ta a kan kimanin N1, 200 a kasuwa a cikin karshen makon nan.

Naira
Naira ta tashi a kan Dalar Amurka a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Naira ta danne Dala a kasuwar canji

Kara karanta wannan

Naira ta gama tashin gishirin Andrew, Dalar Amurka ta sake harbawa a Najeriya

Rahoton Nairametrics ya ce masu kasuwancin kudin kasashen ketaren sun tabbatar da an samu sauki a kan farashin Dalar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka kamanta da abin da aka saida Dala a ranar Juma’a, kudin Najeriyan na Naira ya tashi da 8.57% watau N120 a kasuwar canji.

‘Yan kasuwa sun ce an yi cinikin Dala ne tsakanin N1, 280 da N1,300 a bayan fage. Naira Rates ta ce an saida Dala a kan N1, 240 a jiya.

Halin da Dala-Naira suke ciki a yau

A tsakiyar makon da ya wuce, Naira ta rasa kaso mai tsoka na darajarta bayan ta tashi zuwa kusan N1, 000 a kan Dala a karon farko.

An yi watanni rabon da a saida ko a saye Dala a kan kasa da N1, 000 a kasuwannin bayan fage ko kuwa manyan bankunan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

Bankin CBN ya rabawa 'yan canji Dala

Daily Trust ta ce hakan ya sa ake tunanin tasirin $15.83m da bankin CBN ya rabawa ‘yan kasuwar bayan fage na BDC fiye da 1,580.

Babban bankin kasar na CBN ya ba ‘yan canji masu lasisi $10, 000 domin rage karancin kudin Amurkan a kasuwannin bayan fage.

Amma sai dai bayanan da ke kafar FMDQ ya nuna Naira ta rage kima ne a jiya domin kuwa an yi cinikin Dala ne a kan N1,339.23.

Faduwar Naira ta sa CBN a matsala

Cikin awanni, Naira ta rasa 2.24% na darajarta domin a kan N1,309.88 kafin nan yayin da gwamnan CBN yake neman gano bakin zare.

Kwanaki bayan Naira ta yi ta tashi har ana murna, yanzu labari ya zo cewa Dala ta koma sukuwa a kan kudin Najeriyan na Naira.

Tun can wasu masana sun ce babu tabbas a kan irin tashin da Naira ta yi, ana tsoron za a koma gidan jiya bayan wasu 'yan kwanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng