Fargaba Yayin da Gwamnan APC Ya Sake Garkame Wuraren Ibada da Shakatawa 19
- Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe wuraren ibada da na shakatawa saboda yawan kararrakin wanda ke shiga hakkin mutane
- Hukumar kula da muhalli a jihar ta tabbatar da kulle coci-coci biyar da wuraren shakatawa akalla 19 da wasu kasuwanni
- Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke zargin wadanda abin ya shafa da shiga hakkin jama'a da saba ka'ida ta muhalli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamnatin jihar Legas ta rufe coci-coci guda biyar da wuraren shakatawa 19 a jihar.
Hukumar kula da muhalli a jihar Legas ta dauki matakin ne saboda yawan damun jama'a da kara da wuraren ke yi.
Musabbabin rufe wuraren ibadun a Legas
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa a jihar, Tokunbo Wahab shi ya bayyana haka a shafinsa na X kan matakin da aka dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wahab ya ce an rufe wuraren ne na wucin gadi zuwa lokacin da za su bi dokokin muhalli a jihar ba tare da saba ka'ida ba.
Har ila yau, hukumar ta rufe wasu kasuwanni hudu da manyan kantuna saboda matsalar kara da kuma saba dokokin muhalli.
Wuraren da abin ya shafa a Legas
Daga cikin coci-coci da aka rufen akwai St Monica’s Hall of Our Lady of Lord’s Catholic da Christ Rock of Fire Ministry da Wonderful Bible Prayer Ministries da God’s Porch Ministries da kuma wani wanda ba a bayyana ba.
Sai wuraren shakatawa da aka kulle sun hada da School2bar da Blue Seasons da Sulerious Lakeside da Monero da otal na Lekki da sauransu.
Gwamnan Legas ya magantu kan karin albashi
A wani labarin makamancin wannan, gwamnatin jihar Legas ta yi martani kan rade-radin karin mafi karancin albashi a jihar.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya karyata jita-jitar cewa ya amince da karin mafi karancin albashi har zuwa N70,000 a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya yi bayanin cewa Gwamnatin Tarayya nan ba da jimawa ba za ta bayyana mafi karancin albashi.
Asali: Legit.ng