Hukumar FRSC Ta Karrama Jami'anta Bisa Dawo da N870m a Kaduna

Hukumar FRSC Ta Karrama Jami'anta Bisa Dawo da N870m a Kaduna

  • Jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) guda huɗu sun samu takardun yabo bisa halin kirki da gaskiya da suka nuna
  • An yabawa jami'an na FRSC ne bisa dawo da Naira miliyan 870 waɗanda suka samu a wajen wani hatsarin mota da ya auku
  • Wasu ƴan Najeriya sun ce kamata ya yi hukumar ta FRSC ta yi wa jami’an ƙarin girma a maimakon ba su takardun yabo kawai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta gabatar da takardun yabo ga jami’anta guda huɗu da suka dawo da Naira miliyan 870 da aka samu a wajen wani hatsarin mota.

Jami’an na FRSC sun gano kuɗaɗen ne a wani aikin ceto a Olam, jihar Kaduna a ranar 24 ga watan Afrilu, 2024 bayan an yi hatsarin mota.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Lauya ya hango kuskuren hukumar EFCC, ya yi gargadi

An karrama jami'an FRSC
An karrama jami'an FRSC a Kaduna bisa dawo da N870m Hoto: @OfficialFRSC
Asali: Twitter

An bayyana hakan ne a wani rubutu da hukumar ta wallafa a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @FRSCNigeria a ranar Juma’a, 26 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun na cewa:

"Gabatar da takardun yabo a madadin Corps Marshal Dauda Ali Biu, zuwa ga jami’an FRSC da suka dawo da kuɗi Naira miliyan 8,700 da aka samu yayin aikin ceto a wani hatsarin mota a Olam, jihar Kaduna a ranar 24 ga watan Afrilu 2024."

Ƴan Najeriya sun yi martani

Wasu ƴan Najeriya sun taya jami'an hukumar murna a shafukan sada zumunta bisa gaskiyar da suka nuna da yabon da suka samu, amma sun buƙaci hukumar ta yi musu ƙarin girma maimakon ba su takardun yabo kawai.

Ga wasu daga ciki nan ƙasa:

@Its_chi ya rubuta:

"A cikin wannan halin matsin tattalin arziƙin kamata ya yi ku yi musu ƙarin girma maimakon ba su wata takarda da ba za ta amfane su da komai ba."

Kara karanta wannan

Bam ya hallaka jami'an CJTF 5 a jihar Borno, wasu sun samu raunuka

"Wannan dalilin ne ya sanya rundunar ƴan sanda ta yi zarra. Ku ƙara musu girma hakan zai ƙarfafa gwiwar wasu su nuna halayya mai kyau."

@Nuris01 ya rubuta:

"Mutumin kirki. Kamata ya yi a ƙara masa girma domin ƙarfafa gwiwa a riƙa samun irin wannan halin."

@PiusLastborn1 ya rubuta

"Mun taya su murna"

@ayocole ya rubuta:

"Aiki ya yi kyau"

An karrama ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta karrama jami’an ta guda huɗu bisa ƙin karɓar cin hancin N8.5m daga hannun wani ɗan bindiga a yayin da suke gudanar da bincike.

Kwamishinan ƴan sandan jihar David Iloyalonomo, ya ba jami’an ƴan sandan gudu huɗu kyauta a ofishinsa dake hedikwatar ƴan sandan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng