Badaƙalar Kuɗin Kwangila: ICPC Ta Cika Hannu da Daraktar TETFund

Badaƙalar Kuɗin Kwangila: ICPC Ta Cika Hannu da Daraktar TETFund

  • Daraktar kudi da kula da asusu ta hukumar bada tallafin karatu ga manyan makarantu (TETFund), Gloria Olota ta kwana a hannun hukumar ICPC
  • ICPC da ke yaki da cin hanci da rashawa ta tsare Mrs Oluto ne kan zargin sa hannunta a badaƙalar kwangilar N3.8 da TETFund ta bayar
  • An ruwaito cewa TETFund ba ta bi ka'ida wajen bayar da kwangilar ba kuma babu wata hujja da ta nuna yadda aikin kwangilar ya gudana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta tsare Gloria Olotu, daraktar kudi da asusu ta hukumar tallafawa manyan makarantu (TETFund).

Kara karanta wannan

Kudin makarantar ƴaƴan Yahaya Bello; makarantar Amurka za ta turawa EFCC $760,910

Hukumar ICPC ta tsare daraktar hukumar TETFund
Badakalar N3.8bn: Daraktar TETFund ta kwana a hannun hukumar ICPC. Hoto: @TETFundNg
Asali: Twitter

ICPC ta tsare daraktar TETFund

Wannan kuwa ya biyo bayan wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar a kwanan baya kan zargin an tafka badaƙalar N3.8bn a kwangilar da TETFund ta bayar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan jami'ai a hukumar ICPC sun bayyana cewa a ranar Alhamis sun gayyaci Mrs Oluto da Kolapo Okunola (daraktan sashen ICT na hukumar) da wani Joseph Odo domin amsa tambayoyi.

Sai dai hukumar ta sallami Okunlola da Odo ne kawai da cewar za su koma ofishin Hukumar ranar Juma'a yayin da ta tsare Mrs Oluto.

Matsayin daraktar a badakalar TETFund

Rahoton da jaridar Premium Times ta fitar na yau Juma'a ya nuna cewa daraktar ta TETFund ta gaza cika sharuddan beli da aka dora mata.

Majiyar ICPC ta shaidawa jaridar cewa sun ayyana sunan Mrs Oluto a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a badaƙalar.

Kara karanta wannan

FAAN ta dauki matakin gaggawa da gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

Mai magana da yawun hukumar da ke yaki da rashawar ta ICPC, Ademola Bakare ya tabbatar da wannan ci gaban a ranar safiyar Juma'a.

Badaƙalar N3,812,500 a hukumar TETFund

A ranar Litinin ne aka ruwaito cewa an tafka badaƙalar kudi da ta kai N3,812,500 a kwangilar da TETFund ta ba Makarantar Fides Et Ratio.

Kamar yadda ya sabawa dokar kasa, TETFund ta biya dan kwangilar N2.9bn a biya hudu, wanda tun asali ba a bi ka'ida wajen bayar da kwangilar ba.

An ce babu wata takarda ko hujja da ta nuna hukumar ta fitar da bayanan bayar da kwangilar kamar yadda dokar ba da kwangila ta tanadar.

Makarantar AISA ta tuntubi EFCC

A wani labarin kuma, makarantar Amurka da ke Abuja ta tuntubi hukumar EFCC kan batun kudin makarantar 'ya'yan Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi.

Makarantar AISA ta nemi ta mayarwa hukumar EFCC $760,910 da Ali Bello ya tura mata na kudin makarantar 'ya'yan Yahaya Bello bayan ta cike kudaden sabis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.