'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Rundunar Sojoji a Jihar Katsina

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Rundunar Sojoji a Jihar Katsina

  • Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa ƴan bindiga sun kashe babban kwamandan sojoji a kauyen Malali, ƙaramar hukumar Kanƙara
  • Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis yayin da yake kan hanyar zuwa kai ɗauki kauyen domin daƙile harin ƴan bindiga
  • Tuni dai aka ɗauki gawarsa bayan musayar wuta, yanzu haka an ajiye gawar a wani asibiti a cikin birnin Katsina

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wani kwamandan rundunar sojojin Najeriya da ke sansanin Sabon Garin Ɗan'Ali a ƙaramar hukumar Ɗan Musa a Katsina ya rasa ransa a harin kwantan ɓauna.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis kuma tuni aka kai gawar marigayin, wanda ya kai matsayin Manjo a gidan soji, wani asibiti a Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 3, sun sace wasu 8 a jihar Kaduna

Manjo Janar Lagbaja.
Mahara sun yi ajalin kwamandan sojoji a jihar Katsina Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro daga majiya mai tushe cewa kwamandan (wanda aka sakaya sunansa), an kai masa harin kwanton bauna ne a kauyen Malali da ke karamar hukumar Kankara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa maharan sun yi ajalin kwamandan yayin da yake kan hanyar zuwa kai ɗauki domin daƙile harin ƴan bindiga a kauyen.

Yadda aka kashe kwamandan sojoji

Wata majiya ta ce:

"Kauyen Malali na kan titin Zangon Pawwa wanda gaba ɗaya ƴan bindiga sun kwace wurin saboda haka duk lokacin da aka kai hari jami'an tsaro kan nemi ɗauki daga sansanin Maraban Dan’Ali.
"Wannan karon sun nemi kwamandan ya kawo musu ɗauki, kawai ya taho a motar Hilux maimakon motar sulke saboda lokacin ba ta nan, kwatsam maharan suka mamaye shi suka harbe shi a kai."

- Majiya

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa lokacin da sojoji suka je ɗauko gawarsa sai da suka yi artabu da ƴan bindigar, a cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Dangin amarya sun nuna jarumta, sun afkawa yan bindiga yayin da suka tare su a Zamfara

"A farko jami'an tsaron sun yi harbi a sama a wurin da ƴan bindigan suke amma da suka ji shiru sai suka matsa gaba. A wannan lokacin ne kwamandan ya ƙariso, suka far masa suka kashe shi," in ji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojojin birged ta 17 a Katsina, Oiza Ehinlaidlye, ba ta ɗaga kiran waya ko amsa sakon tes da aka tura mata ba.

Ƴan bindiga sun baƙunci lahira

A wani rahoton kun ji cewa gwarazan sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga uku tare da ƙwato miyagun makamai a jihohin Kaduna, Sakkwato da Filato.

A wata sanarwa da rundunar sojoji ta fitar, ta ce jami'anta sun samu wannan nasara ne ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262