Katsina: An Shiga Makoki Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban APC da Wani Mutum

Katsina: An Shiga Makoki Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban APC da Wani Mutum

  • Ana cikin fargaba bayan 'yan bindiga sun farmaki wasu mutane biyu tare da yin ajalinsu a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya
  • Harin ya rutsa da wani shugaban jam'iyyar APC a yankin Mai Dabino da ke karamar hukumar Danmusa a jihar
  • Marigayin Sa'idu Basa ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyar Mai Dabino bayan dawowa daga ganawar jam'iyyar a Danmusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Katsina inda suka hallaka mutane biyu.

Maharan sun yi ajalin shugaban jam'iyyar APC a gundumar Mai Dabino a karamar hukumar Danmusa da ke jihar.

Shugaban APC ya gamu da ajalinsa yayin harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan bindiga sun kai hari tare da hallaka mutum 2 ciki har har da jigon APC a Katsina. Hoto: Dikko Umar Radda.
Asali: Facebook

Yaushe 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC?

Kara karanta wannan

Ganduje: Mummunar zanga zanga ta barke a sakatariyar APC kan shugaban jam'iyya

Marigayin Sa'idu Basa ya gamu da ajalinsa ne a ranar Laraba 24 ga watan Afrilu da misalin karfe 3:30 na yammaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne yayin da Basa ke dawowa daga ganawar masu ruwa da tsakin jam'iyyar a Danmusa.

The Guardian ta tattaro cewa jigon jami'yyar ya dauki wani fasinja zuwa Mai Dabino inda suka ci karo da 'yan bindiga.

Gamuwarsu ke da wuya miyagun suka harbe su gaba dayansu inda suka ce ga garinku nan take.

An gudanar da sallar jana'izarsu a Katsina

Tuni aka yi sallar jana'izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya koyar a jiya Laraba 25 ga watan Afrilu, cewar Katsina Reporters.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Abubakar Aliyu bai amsa tuntubar da 'yan jaridu suka yi masa ba kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa

Har ila yau, shi ma shugaban jam'iyyar APC a jihar, Sani Daura bai yi martani kan lamarin da ya yi ajalin jigon jami'yyar ba.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari fadar Sarkin Zurmi a jihar Zamfara.

Maharan sun kutsa kai cikin fadar Sarkin inda jami'an tsaro suka yi nasarar tserewa da shi birnin Gusau yayin harin.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba 24 ga watan Afrilu inda suka hallaka mutane uku tare da lalata karfunan sabis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.