An Tafka Babban Rashi Yayin da Tsohon Sanata Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 66

An Tafka Babban Rashi Yayin da Tsohon Sanata Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 66

  • An tafka babban rashi bayan sanar da mutuwar tsohon Sanata Ayogu Eze da ya wakilci Enugu ta Arewa a Majalisar Dattawa
  • Marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 25 ga watan Afrilu a birnin Tarayya Abuja bayan fama da jinya wacce ba a bayyana ba
  • Tsohon sanatan ya wakilci Enugu ta Arewa daga shekarar 2007 zuwa 2011 inda ya rike mukamin shugaban kwamitin ayyuka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - An shiga jimami bayan sanar da mutuwar tsohon Sanata a jihar Enugu, Ayogu Eze.

Marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 25 ga watan Afrilu a birnin Tarayya Abuja bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa

Tsohon Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Tsohon Sanata a jihar Enugu, Ayogu Eze ya mutu ya na da shekaru 66. Hoto: @MissObikwe.
Asali: Twitter

Yaushe sanatan na Enugu ya rasu?

Eze wanda ya wakilci Enugu ta Arewa daga shekarar 2007 zuwa 2015 ya mutu ne ya na da shekaru 66 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haifi Marigayi Eze a ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 1958 a jihar, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Ya ba da gudunmawa wurin yin wasu sauye-sauye a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska.

Sanatan wanda ya shafe shekaru takwas a Majalisar ya na daga cikin mambobin kwamitin gyara kundin tsarin mulkin Najeriya, cewar The Guardian.

Daga bisani bayan ya sake dawowa Majalisar a karo na biyu a shekarar 2011, ya samu mukamin shugaban kwamitin ayyuka.

Yadda sanatan ya yi fama da jinya

Wata majiya ta tabbatar da cewa sanatan ya gamu da rashin lafiyar wanda har ya hana shi halartar bikin 'yarsa da aka gudanar.

Kara karanta wannan

An yi rashin jarumin fina finai kwanaki da rasa Daso a duniyar wasan kwaikwayo

An yi bikin 'yar marigayin ne a jihar Legas a farkon wannan shekara da muke ciki.

Sanatan ya na daga cikin wadanda suka ba da gudunmawa a PDP tun farkon dawowa dimukradiyya a 1999.

Daga bisani sanatan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC inda ya tsaya takarar gwamnan jihar a shekarar 2019.

Tsohon gwamnan Yobe ya rasu

A wani labarin, an ji cewa tsohon gwamnan jihar Yobe kuma sanata, Bukar Abba Ibrahim ya rasu ya na da shekaru 73 a duniya.

Idan za a tuna, marigayin ya rasu ne a ƙasar Saudiyya bayan ya sha fama da jinya a ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.