Wahalar Fetur: Kwamitin Ko Ta Kwana Ya Fara Aiki Kan Gidajen Mai a Jihar Jigawa
- Biyo bayan dogayen layuka da suka bayyana a gidajen mai, kwamitin ko ta kwana ya fara zaga gidajen mai a jihar Jigawa
- Gwamnatin jihar ta ce ta kafa kwamitin ne domin bincike da ladabtar da gidajen mai da suke boye mai ko kara masa kudi
- Amma a tattaunawar da Legit ta yi da mazauna jihar sun ce basu gani a kasa ba, domin gidajen mai suna cin karen su ba babbaka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Biyo bayan tsadar man fetur da boye shi da ya kunno kai a Najeriya, gwamnatoci sun fara daukan matakai domin warware matsalar.
A jihar Jigawa, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin kota kwana da zai rika tabbatar da cewa gidajen mai suna sayarwa ga al'umma a kowane lokaci.
Fetur: Kwamitin zai yi aiki babu sabo
A wani bayani da mai taimakawa gwamnan jihar a kan harkokin sadarwa, Garba Muhammad, ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna cewa kwamitin ya fita bakin aiki gadan-gadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau Alhamis ne shugaban kwamitin kuma kwamishinan kasa na jihar Kanal Muhammad Alhassan mai ritaya ya jagoranci tawaga domin zagawa gidajen mai.
Aikin kwamitin a kan sha'anin man fetur
Kwamitin ya zaga gidajen mai domin hukunta waɗanda suke boye mai, kara masa kudi ko kin sayar da shi a fadin jihar. Kwamitin kota kwana ya fara aiki kan gidajen mai a jihar Jigawa
A cewar sanarwar, kwamitin zai cigaba da shiga lungunan jihar domin tabbatar da cewa mai ya wadata a fadin jihar.
Har yanzu ana kulle gidajen mai a Jigawa
A tattaunawar da Legit ta yi da wani mazaunin Dutse, Musa Hassan, ya ce lalle su har yanzu basu san da dokar ba. Domin a cewarsa har yanzu gidajen mai sun cigaba da kullewa.
Ya kuma kara da cewa har yanzu kudin mai ya cigaba da haurawa a fadin jihar sakamakon kulle gidajen mai da rashin sayar da shi.
Ya kara da cewa a yanzu ana sayan lita a N900 zuwa N1,000. Saboda haka ko masu achaba sun sayi mai ba sosai suke iya cire kudin ba.
A karshe, Malam Hassan ya yi kira ga gwamnatin da ta tausayawa talakawa ta dauki dokar da gaske domin tsadar mai din ta jawo kudin ababen hawa ya karu sosai.
Wahalar fetur ya jawo layuka sun bayyana
A wani rahoton, kun ji cewa, an wayi garin Alhamis da ganin dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja
Rashin samun man ya kara ta'azzara farashin ababen hawa yayin da wasu gidajen man su ka ki budewa ballantana su sayarwa masu bukata
Sakataren kungiyar masu kasuwancin man fetur ta kasa (IPMAN), John Kekeocha, ya ce za su zauna da kamfanin mai na NNPCL domin gano bakin matsalar
Asali: Legit.ng