Kasar Saudiya ta Sauke Kabakin Arzikin Dabino ga Mazauna Kano

Kasar Saudiya ta Sauke Kabakin Arzikin Dabino ga Mazauna Kano

  • Kasar Saudiyya ta raba tallafin dabino masu tarin yawa ga masallatai, marasa lafiya, marayu da sauran marasa galihu a jihar Kano
  • Sakataren gwamnatin Kano, Baffa Bichi ne ya karbi katan dubu 3 na dabinon, kuma ya yi godiya kan goma ta arzikin da ake musu
  • Jakadan Saudiya a karamin ofishin jakandinsu na Kano, Khaleel Ahmad Adamawiy ya ce kasarsa na taimakon Najeriya ta fuskoki da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano - Kasar Saudiya ta tallafawa masallatan juma’a, makarantun Islamiyya, marayu da marasa lafiya da ke jihar Kano da dabino katan dubu uku.

Karamin ofishin jakandancin kasar a Kano ne ya mikawa gwamnatin jihar dabinon wanda sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya karba a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Gidauniyar Sarkin Saudiyya ta raba katan dubu 3 a Kano
Gidauniyar ta raba dabinon ne ga mabukata a Kano Hoto:His Majesty King Mohammad bin Salman bin Abdulaziz Al Saud/DATES- A Wonder Fruit of Arabia
Asali: Facebook

Kyautar gwamnatin Saudiyya a Najeriya

Sakataren gwamnatin Kano, ya ce kasar Saudiya ta dade ta na bayar da tallafi ta fuskoki da dama a jihar Kano, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa;

“Mu na godiya ga Allah SWT kan wannan tallafi da sauran taimakon da gwamnati da al’ummar kasar Saudiyya ke ba mu.”

Baffa Bichi ya bayar da tabbacin mika dabinon ga wadanda aka bayar dominsu.

“Saudiyya na tallawa Najeriya sosai,” Khaleel

Da ya ke mika dabinon ga gwamnatin Kano, karamin jakadan Saudiyya a Kano, Khaleel Ahmad Adamawiy ya ce gwamnatin kasar ta gidauniyar Sarki AbdulAziz na tallafawa Najeriya ta fuskoki da dama.

Daga irin tallafin da kasar Saudiyar ke bayarwa akwai ba mutane 48,300 a jihohin Kano da Yobe da Borno wanda aka kashe kusan $500,000.

Khaleel Ahmad Adamawiy ya kara da cewa haka kuma su na bayar da taimako a bangaren lafiya a Abuja, Kano da Legas, kamar yadda jaridar The Sun ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamatin Sokoto ta tumbuke hakimai 15, an canzawa wasu masarautu

Saudiyya ta yi wa Kano goma ta arziki

Mun ruwaito mu ku a baya cewa gidauniyar Sarki Salman Ibn AbdulAziz ta raba kayan abinci iyalai fiye da 2,000 a jihar Kano a kananan hukumomi takwas da ke jihar.

Daga irin abincin da aka raba akwai shinkafa, da wake da gari, a wani yunkuri na taimakawa mabukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.