JAMB: Dalibai Miliyan 1.5 ba Za Su Samu Shiga Manyan Makarantu ba Inji Gwamnati
- Gwamnatin tarayya ta bayyana adadin daliban da su ka rubuta jarrabawar UTME da za su samu guraben karatu a manyan makarantu
- Ministan ilimi na kasa, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan, inda ya ce kaso 20% ne kawai za sus amu guraben karatun
- Ya ce koyon aikin hannu ne daya daga mafita daga rashin samun guraben karatun tsakanin dubban daliban da ke neman guraben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kaso 20% cikin wadanda za su rubuta jarrabawar shiga makarantar gaba da sakandare ta UTME ne za su samu guraben karatu a jami'o'i da sauran manyan makarantu a Najeriya.
Ministan ilimi na kasa, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zagayen duba yadda jarrabawar UTME ke gudana tare da shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun, Farfesa Ishaq Oleyede.
Ministan ya kara da cewa karancin guraben karatu a manyan makarantun ne ya janyo dole kadan ne daga dalibai kimanin miliyan 1.9 da ke rubuta jarrabawar ne za su samu guraben karatun, kamar yadda Premium times ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya shawarci koyawa dalibai aikin hannu
Ministan ilimin, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana damuwa kan yawan daliban da ke neman guraben karatu, kuma babu su.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, Ministan na ganin koyawa matasan kasar nan ayyukan hannu zai taimaka wajen hana zaman kashe wando idan ba su samu guraben karatun ba.
A cewarsa, kamata ya yi a dora yara kan gwadaben koyon aikin hannu da zarar sun fara karatu, domin hakan zai taimaka musu a rayuwarsu.
A ganinsa, idan yara su ka koyi sana'o'in hannu, ana kyautata zaton da zarar sun kammala sakandare za su iya dogaro da kansu ba tare da sun zama matsala ga iyayensu ko sauran al'uma ba.
Gwamnati za ta kayyade shekarun shiga jami'a
Bayan ganewa idanunsa yadda dalibai masu shekaru 15-16 ke rubuta jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB), Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya ce gwamnatin tarayya za ta kayyade shekarun shiga jami'a.
Ministan ya ce abun damuwa ne yadda kananan yaran ke rubuta jarrabawar saboda yadda iyayensu su ka matsa sai sun rubuta jarrabawar da kananan shekaru.
Asali: Legit.ng