Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada

Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada

  • Wani mutumin kasar Ghana da ke zama a kasar Kanada ya haddasa cece-kuce a yanar gizo bayan ya bayyana yadda ya samu damar komawa kasar waje da zama
  • A wata hira da aka yi da shi, mutumin ya bayyana cewa ya yi danasanin rashin koyon sana’ar hannu a tsawon rayuwarsa a Ghana domin shine abun da ake nema ruwa a jallo
  • Mutane da dama da suka ga wallafar sun nuna rashin jin dadi cewa yawancin matasa sun fi son aikin ofis fiye da aikin hannu

Wani mutumin kasar Ghana mai suna Ben Sey ya magantu game da yadda rayuwarsa ta kasance bayan ya yi kaura daga Ghana inda ya ce ya yi danasanin rashin koyon sana’ar hannu kafin ya koma kasar waje da zama domin da shi ake kudancewa a kasar Kanada.

Kara karanta wannan

Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30

Da yake tuna halin da ya tsinci kansa, matashin ya kuma bayyana cewa ya yi karatu har zuwa matakin gaba da sakandare a Takoradi Polytechnic inda ya mallaki HND a bangaren zane-zane sannan ya samu damar tafiya waje bayan wasu shekaru.

Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada
Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada Hoto: SVTV Africa/YouTube
Asali: UGC

Suna bukatar mutane masu aikin hannu

Ya bayyana cewa yawancin mutanen da ake bibiya a aikin da yake yi a yanzu sune wadanda ke da gogewa a harkar sannan ya yi danasanin cewa bai taba koyon aikin hannu ba a Ghana.

Mutanen da suka karanta wallafar sun magantu sosai kan lamarin. Tuni labarin ya hada sharhi kusan 5,000 da kuma martani sama da guda 100.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Farouk FK ya ce:

“Na tuna lokacin da na yanke shawarar zama injiniyan kanikanci abokaina na ta tsokana na. wasu na ta kirana sunaye amma a yau na zama babban injiniya kuma babu wanda zai iya dauke hakan daga gareni kuma ina matukar farin ciki da kasancewa haka."

Kara karanta wannan

Za mu kwamushe shi: Za a yi maganin wani dan sandan da aka ga yana busa taba a bainar jama'a

Kofi Atta Djan ya yi martani:

“Wannan ne dalilin da yasa nake tausayawa iyaye da dama da ke asarar kudinsu wajen tura yaransu makaranta… saboda na san 90% dinmsu ba za su samu aiki ba a karshe."

Yaw Jonas ya ce:

“Ghana kadai ce kasar da bata dauki makarantar fasaha da muhimmanci ba. Kada ka damu yallabai, ina tare da kai."

Kwame Boateng ya rubuta:

“Koda kai mai aski ne ko mai gyaran gashi a wadannan kasashe kana samun kudi sosai fiye da aikin ofis."

Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30

A wani labari na daban, wani mai amfani da shafin Twitter ya bayyana aure a matsayin damfara yayin da ya tuna yadda ya bata shekaru 30 na rayuwarsa yana zaune da matar da ya kira da “shaidaniya.”

A wani wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, mutumin ya ce ya kama matarsa ta shekaru 30 tana cin amanarsa tare da wani saurayinta na makarantar sakandare shekaru biyu da suka shige.

Kara karanta wannan

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

Mutumin ya bayyana cewa lamarin ya tursasa masa barin gidan aurensa inda ya koma zama a wani gida mai daki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel