An Shiga Jimami Yayin da Tsohon Sarki a Yobe Ya Rasu a Saudiyya a Shekaru 82
- An shiga jimami bayan rasuwar tsohon Sarkin Damaturu a jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya
- Tsohon Sarkin a jihar Yobe ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya a kasar Saudiyya ya na da shekaru 82 a duniya
- Sakataren Hukumar Alhazai, Usman Mai Aliyu Biriri ya tabbatar da mutuwar tsohon Sarkin ga manema labarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Saudiyya - Sarkin Damaturu a jihar Yobe na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.
Marigayin ya rasu ne a kasar Saudiyya bayan ya sha fama da jinya ya na shekaru 82 a duniya.
Yaushe marigayin ya riƙe Sarkin Damaturu?
An nada marigayin a matsayin Sarkin Damaturu a watan Agustan 1993 kafin cire shi a mulkin soja a shekarar 1995.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya taɓa riƙe kwamishinan kudi a jihar Borno lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a 1984.
Daily Trust ta tattaro cewa Mai martaba Biriri ya rasu ya bar mata daya da yara da yawa a kasar Saudiya bayan fama da jinya.
Sanarwar rasuwar marigayin daga iyalansa
Sakataren Hukumar alhazai a jihar Yobe, Usman Mai Aliyu Biriri ya tabbatar da mutuwar marigayin.
"Tabbas ya rasu, a maganar da muke yi yanzu mu iyalansa muna ci gaba da karbar gaisuwa daga jama'a, zan yi magana da ku daga baya lokacin da ya dace."
- Usman Mai Aliyu Biriri
Usman yayin sanar da mutuwar, ya ce marigayin ya rasu ne a wani asibitin Saudiyya inda ta ce za a sanar da lokacin sallar jana'iza a masallacin Makkah.
Kafin rasuwarsa, Biriri ya rike mukamin kwamishinan tarayya a Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) na tsawon lokaci.
Babban Basarake a Ondo ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa an tafka babban rashi a jihar Ondo bayan rasuwar fitaccen basarake da ake kira Olojoda na Oda.
Marigayin mai suna Julius Omomo ya rasu ne ya na da shekaru 83 a duniya bayan ya sha fama da jinya.
Wani daga cikin iyalan basaraken, Ade Adelakun shi ya bayyana mutuwar Sarkin a yau Lahadi 14 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng