70% na Fursunoni a Kano Suna Zaman Jiran Shari'a Ne, Suna Samun Ilimi a Daure
- Hukumar kula da gidajen yari a Kano ta ce kaso 70% na daurarrun dake jihar na jiran tsammanin a gurfanar da gaban kotu
- Jami'in hulda da jama'a na hukumar a Kano, Musbahu Lawan ya shaidawa manema labarai cewa ana fuskantar cunkoso a gidajen
- Ya ce daurarrun su na samun horon ilimi inda da yawa su ka yi nasara a jarrabawar SSCE, kuma su na neman shiga jami'ar NOUN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- Ofishin hukumar kula da gidajen yari na kasa reshen Kano, ya ce kimanin kashi 70% na fursunonin da ke tsare, wadanda ke jiran shari’a ne.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan, da ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin, ya ce cunkoson da ake da shi a gidajen gyaran-hali babban kalubalen ne ga ma’aikatan hukumar.
Ya ce yawan wadanda ke jiran shari’a sun ninka wadanda aka yankewa hukunci har sau uku a jihar Kano, kamar yadda The Guardian ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in ya ce ma’aikata sun fi jin dadin sarrafa wadanda aka yankewa hukunci daga cikin masu laifin da ke tsare, tun da wajibi ne su bi dokokin da gidajen gyaran hali suka tsara, ba kamar masu jiran shari’a ba.
“Muna ilimantar da daurarru,” Musbahu
A karin bayanin da kakakin hukumar, Musbahu Lawan ya yi, ya ce ce ana ilimantar da daurarrun da ke gidajen ajiya a Kano.
A cewarsa, daurarru da dama sun rubuta jarrabawar kammala sakandare kuma sun yi nasara sosai, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.
Ya ce:
“Da yawa daga wadanda aka yankewa hukunci na cin moriyar shireye-shiryen ilimi a gidajen ajiyar. Misali, daurararu kimanin 38 sun rubuta jarrabawar NECO SSCE kuma yanzu haka su na neman shiga Jami’ar karatu daga nesa ta NOUN.”
Jami'in ya kara da cewa kasancewar daurarrun na nuna sha’awar zurfafa karatu ya sa su ke kokarin ganin NOUN ta bude karin wuraren karatu a gidajen ajiya da gyaran halin.
An garkame mutane 300 a Kano
Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cewa kimanin mutane 300 ne aka garkame su a gidan gyaran hali ba tare da an tuhume su ba.
Wannan, ya biyo bayan bincike da Sufeta Janar na rundunar, Kayode Egbetokun, ya umarci a gudanar.
Asali: Legit.ng