Badakalar Kudi: Hukumar EFCC Ta Tsare Mai Neman Takarar Gwamnan Jihar Ondo

Badakalar Kudi: Hukumar EFCC Ta Tsare Mai Neman Takarar Gwamnan Jihar Ondo

  • Wale Akinterinwa, tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Ondo, yanzu haka yana hannun hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci
  • An tattaro cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan na tsare da Akinterinwa ne bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jihar
  • Akinterinwa, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon Gwamna Rotimi Akeredolu, yana ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamna a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta tsare wani ɗan takarar gwamna na zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar Ondo, Wale Akinterinwa.

Akinterinwa dai yana hannun hukumar EFCC ne a bisa binciken da ake yi kansa na kujerar kwamishinan kuɗi da ya riƙe na shekara bakwai a lokacin mulkin tsohon gwamna Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Farfesa tare da sace mutum 2 a wani sabon hari

EFCC ta tsare Wale Akinterinwa
Akinterinwa na tsare a hannun EFCC Hoto: Akinterinwa Media Team, EFCC
Asali: Facebook

Akinterinwa a hannun jami'an EFCC

Jaridar The Nation ta ce wata majiya da ta zanta da manema labarai kan lamarin ta bayyana cewa ana binciken tsohon kwamishinan ne bisa zargin almundahanar biliyoyin Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta gayyaci Akinterinwa a makonnin da suka gabata domin tattaunawa kan wasu zarge-zarge amma bai mutunta gayyatar ba sai ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilun 2024, cewar rahoton Politics Nigeria.

A cewar majiyar:

"A makonnin da suka gabata, EFCC ta gayyaci Akinterinwa domin yi masa tambayoyi kan wasu batutuwa a lokacin da yake kwamishinan kuɗi. Amma bai amsa gayyatar ba."
"Hukumar na da zaɓin bayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, amma ta haƙura saboda kada siyasa ta shigo ciki domin yana takarar gwamna a zaɓen fidda gwanin jam'iyyar APC."
"Amma Akinterinwa ya kawo kansa ga hukumar EFCC a Abuja. An tsare shi domin yi masa tambayoyi."

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin addinin da 'yan bindiga suka sace ya shaki iskar 'yanci

“Akinterinwa yana tsare a hannunmu. Ba mu kamo shi ba, shi ne ya kawo kansa bisa gayyatar da muka yi masa tun kwanaki. Ina baka tabbaci cewa tsare shi baya da alaƙa da siyasa."

EFCC na neman Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan na neman Yahaya Bello ne bisa laifuffukan da suka shafi almundahanar maƙudan kuɗaɗe

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng