'Yan Sanda Sun Sheke Dan Bindiga Tare da Cafke Wasu 2 Za Su Kai a Katsina
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun samu nasara kan ƴan bindiga
- Jami'an tsaron sun sheƙe ɗan bindiga ɗaya tare da cafke wasu miyagun biyu bayan sun yi yunƙurin kai hari a ƙauyen Madachi na ƙaramar hukumar Sabuwa
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa inda ya ƙara da cewa an ƙwato babura guda biyu a hannun tsagerun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wasu ƴan bindiga mutum biyu a jihar.
Jami'an rundunar ƴan sandan sun cafke ƴan bindigan ne lokacin da suka yi yunƙurin kai hari a ƙauyen Madachi, cikin ƙaramar hukumar Sabuwa.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 21 ga watan Afirilun 2024, cewar rahoton tashar Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka cafke 'yan bindigan
Kakakin ya bayyana cewa jami'an ƴan sandan sun samu nasarar daƙile harin ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Afirilu tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Aliyu ya ƙara da cewa jami'an tsaron sun kuma hallaka ɗan bindiga ɗaya tare da ƙwato babura guda biyu a yayin fafatawar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ƴan bindiga sun buɗe wuta kan tawagar jami'an tsaro yayin da suke aikin sintiri bayan sun isa ƙauyen Madachi na ƙaramar hukumar Sabuwa a ranar 19 ga watan Afirilu, 2024, da misalin ƙarfe 9:00 na safe."
"Cikin nuna ƙwazo tawagar jami'an tsaron ta yi ruwan wuta tare da samun nasarar daƙile harin da cafke mutum biyu da ake zargi."
"A yayin da ake duba wurin da aka yi artabun, an gano gawar ɗan bindiga ɗaya da babura guda biyu da ƴan bindigan suke amfani da su."
Ƴan bindiga sun sace mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutane 28 a kauyen Zamfarawar Madogara da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kuma sace aƙalla mutane 20 galibi mata da ƙananan yara ƴan bindiga suka sace daga kauyen Na-Alma da ke ƙaramar hukumar Malumfashi.
Asali: Legit.ng