An Shiga Jimami Bayan Fasinjoji Sun Kone Kurmus a Wani Hatsarin Mota a Kogi
- An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota da ya salwantar da rayuka a garin Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi
- Hatsarin wanda ya auku bayan wasu motocin bas guda biyu sun yi taho mu gama, ya jawo fasinjojin da ke cikin motocin sun ƙone ƙurmus
- Babu wanda ya tsira daga cikin motocin bayan an kasa kashe gobarar da ta tashi saboda rashin kayan kashe gobara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Wasu mutane sun ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsari da ya auku a Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi, da safiyar ranar Lahadi.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa hatsarin wanda ya auku a gaban kwalejin koyarwa ta Aloma, ya ritsa da motocin bas guda biyu da wata tirela.
Yadda hatsarin ya auku
Majiyar ya ce wata motar bas ƙirar Sienna wacce ke cike da fasinjoji ta yi karo da wata motar bas ƙirar Toyota da ke tahowa a ƙoƙarin kaucewa ramin da kan titi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Motocin biyu na haɗewa kawai sai suka kama da wuta nan take, wanda hakan ya jawo dukkan mutanen da ke cikin motocin suka ƙone.
Wani mazaunin garin Aloma, Adejo Usman ya bayyana cewa:
"Dukkan fasinjojin da ke cikin motar Toyota, ciki har da direban sun ƙone ƙurmus.
"Waɗanda ke cikin motar Sienna suma sun ƙone, babu wanda ya tsira. Wata mota da ta tsaya a kusa da wurin da lamarin ya faru ita ma ta kama wuta inda ta ƙone ƙurmus. Gobarar ta kuma lalata wani gida da ke kusa da wurin.
"Har yanzu ba mu tabbatar da wani wanda ya tsira da ransa ba, face waɗanda ke cikin motar da aka ajiye a kusa da wurin"
Ya ce mutanen ƙauyen ba su iya yin komai don ceto wasu fasinjojin da suka maƙale ba saboda babu kayan kashe gobara, rahoton jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Kwamandan sashi na hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) Samuel Ayedeji, ya ce yana cikin wani taro ne a lokacin da aka tuntuɓe shi kan lamarin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, bai ɗauki kiran da aka yi masa ta waya ba, sannan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Mutum 13 sun mutu a hatsarin mota
A wani labarin kuma, kun ji cewa Akalla mutane 13 suka mutu, wasu 40 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kan titin Ahmadu Bello, a cikin birnin Kaduna.
Lamarin ya auku ne bayan wata motar tirela da ke jigilar fasinjoji da albasa daga Kano ta kwace tare da afkawa kan wata motar da ke tafiya
Asali: Legit.ng