Kungiyar Kwadago Ta Lissafo Sabbabin Bukatu Guda 7 Ga Gwamnatin Tarayya da Na Jihohi

Kungiyar Kwadago Ta Lissafo Sabbabin Bukatu Guda 7 Ga Gwamnatin Tarayya da Na Jihohi

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta aika da sababbin buƙatu guda bakwai ga gwamnati waɗanda take so a biya mata su
  • Ƙungiyar na neman a samar da ƴan sandan jihohi da na ƙananan hukumomi domim tunkarar matsalar rashin tsaro
  • Ma'ajin ƙungiyar NLC na ƙasa, Hakeem Ambali wanda ya zayyano buƙatun ya kuma ƙara da batun aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gabanin ranar ma’aikata ta 1 ga watan Mayu, 2024, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta lissafa wasu bukatu guda bakwai da take so gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta cika.

Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma gabatar da wasu buƙatu ga gwamnatocin jihohi.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindinga sun kashe 'yan banga 3 tare da sace mutane masu yawa a wani sabon hari

Kungiyar kwadago ta mika sababbin bukatu
Kungiyar kwadago na son a samar da 'yan sandan jihoji Hoto: @DOlusegun, @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

A cikin rahoton da jaridar The Punch ta fitar a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu, ta ce Hakeem Ambali, ma'ajin ƙungiyar NLC na ƙasa, ya lissafo buƙatu bakwai da ƙungiyar ta gabatar ga gwamnatin tarayya da na jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane buƙatu NLC ta gabatar?

"Da farko, muna sa ran a samar da dangantaka mai kyau tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati tare da cikakken aiwatar da mafi ƙarancin albashi a matakin ma’aikatan tarayya, jihohi, ƙananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu."
"Biyan basussukan kuɗaɗen ƴan fansho. Samar da cibiyoyin sauya iskar gas a dukkanin mazaɓun sanatoci, gyara matatun man fetur na Kaduna da Fatakwal.
"Samar da ƴan sandan jihohi da na ƙananan hukumomi, ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu, da ba su gudunmawar da ta dace wajen samar da abubuwan more rayuwa."

Kara karanta wannan

An sheke shugabannin 'yan bindiga 2 a wani kazamar fada a jihar Zamfara

- Hakeem Ambali

Ga cikakken jerin buƙatunsu a nan ƙasa:

1. Samar da ƴan sandan jihohi da na ƙananan hukumomi

2. Ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu

3. Kyakkyawar fahimtar juna tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati

4. Aiwatar da mafi ƙaranci albashi

5. Biyan kuɗaɗen ƴan fansho

6. Samar da cibiyoyin sauya iskar gas

7. Gyara matatun man fetur na Fatakwal da Kaduna

Batun mafi ƙarancin albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta gabatar da N709,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.

A ɗaya bangaren kuma kungiyar ƴan ƙwadago (TUC) ta bada shawarar N447,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng