Matsalar Tsaro Ta Ta’azzara a Filato, an Rufe Jami’ar Jihar Bayan Kashe Dalibi
- Mahukuntan jami'ar jihar Filato da ke Bokkos, sun rufe jami'ar tare da dakatar da jarabawar karshen zango da dalibai ke zanawa
- Rufe jami'ar ya biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Chikam da ke kusa da jami'ar inda aka kashe dalibi dan aji biyu
- Zainab Mohammed Dass, shugabar dalibai a jami'ar Abuja a yayin zantawa da Legit Hausa ta koka kan yadda matsalar tsaro ta addabi Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bakkos, jihar Filato - A ranar Juma'a ne magatakardar jami’ar jihar Filato, Yakubu Ayuba ya sanar da cewa an dakatar da karatu a jami'ar da ke karamar hukumar Bokkos.
Matsalar tsaro: An rufe jami'ar Filato
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai wani farmaki kauyen Chikam da ke kusa da jami'ar inda aka kashe dalibin aji biyu a jami'ar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wannan sanarwar da ya fitar, Ayuba ce:
"Hukumar gudanarwar jami'ar ta dauki matsaya ta rufe jami’ar na tsawon kwanaki goma daga yau 19 ga Afrilu, 2024.
"Wannan ya biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a jami'ar jihar Filato ta Bokkos da kauyukan da ke kewaye da ita a ranar Juma'a 19 ga Afrilu 2024."
An dakatar da jarabawar karshen zango
Jaridar The Punch ta rahoto Ayuba ya ce matakin rufe jami'ar zai ba dalibai kariya daga hare-haren 'yan bindiga tare da kuma neman hanyar inganta tsaro kafin a dawo karatu.
Ya ce jami'ar ta dakatar da dukkanin jarabawar karshen zangon karatu na farko da dalibai ke zanawa a halin yanzu har zuwa ranar Alhamis 2 ga watan Mayu, 2024.
Magatakardar ya kara da cewa:
"Mahukuntan makarantar sun samar da motoci da A su yi jigilar dalibai daga jami'ar zuwa Barkin Ladi daga ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu."
Gwamna Mutfwang ya magantu kan harin
A hannu daya, jaridar Vanguard ta ruwaito Gwamna Caleb Mutfwang ya nuna bacin rai kan sabon harin da aka kai jam'iar da kauyukan da ke makwabtaka da ita.
Gyang Bere, daraktan yada labarai na gwamnan ya fitar da wata sanarwa a ranar Juma’a, inda ya ruwaito Mutfwang ya yi kira da a kara inganta tsaro domin kare rayukan al'ummar yankunan.
Dalibai sun koka kan matsalar tsaro
Zainab Mohammed Dass, shugabar dalibai a jami'ar Abuja ta koka kan yadda matsalar tsaro ke kokarin gurgunta harkar koyo da koyarwa a kasar.
Zainab ta yi misali da shiyyar Arewa maso Gabas da ta fito tana mai cewa 'yan Boko Haram ne suka fara lalata makarantu, wanda ya jawo yawan yara marasa zuwa makaranta.
A cewar ta, matsalolin 'yan ta'adda sun fi yawa a Arewa inda kuma aka fi samun yawan yara marasa zuwa makaranta, tana mai kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa.
Ta ce wannan lamari ba wai ya shafi iya gwamnatin tarayya bane kawai, dole ne gwamnoni su tashi tsaye su kare makarantu a jihohin su.
Filato: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'an tsaro da suka hada da hukumar DSS, 'yan sanda da 'yan banga sun kashe 'yan bindiga masu kai masu kwarmato a jihar Filato.
Wannan kuma ya biyo bayan wani samame da jami'n suka kai wata mabuyar 'yan bindigar a lokacin da suke wani taron tattaunawa, farmaki da ya yi silar kashe 'yan bindiga 18.
Asali: Legit.ng