Za a Iya Tsige Ganduje Daga Ofis Kamar Oshiomhole? APC Ta Yi Karin Haske

Za a Iya Tsige Ganduje Daga Ofis Kamar Oshiomhole? APC Ta Yi Karin Haske

  • APC ta yi bayani kan dalilin da ya sa ba za a tsige Abdullahi Ganduje daga shugaban jam'iyyar ba kamar yadda aka tsige Adams Oshiomhole
  • Sakataren yaɗa labarai na APC, Felix Morka ya ce halastattun 'ya'yan jam'iyyar ne suka tsige Oshiomhole akasin abin da ya faru da Ganduje
  • Morka ya ce wadanda suka sanar da tsige Ganduje ba 'ya'yan jam'iyyar bane, kuma ba su da wani hurumi da ya basu ikon aikata hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Felix Morka ya yi magana kan turka-turkar da har yanzu ake yi kan batun tsige Abdullahi Ganduje daga shugaban jam'iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

APC ta yi magana kan tsige Ganduje daga ofis kamar yadda aka yi wa Oshiomhole
APC ta ce wadada suka sanar da tsige Ganduje ba halastattun 'ya'yan jam'iyyar bane. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Original

Morka ya shaida wa 'yan Najeriya cewa kuskure ne ayi tunanin halin da Ganduje yake ciki a yanzu iri daya ne da wanda Adams Oshiomhole ya shiga lokacin yana shugaban jam'iyyar.

Da wannan, sakataren yaɗa labaran ya ce jam'iyyar ba za ta iya tsige Ganduje daga kujerarsa ba kamar yadda ta tsige Oshiomhole a baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka tsige Oshiomhole daga ofis

Morka ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, lokacin da yake amsa tambayoyi kan batun tsige Ganduje daga shugaban jam'iyyar.

Idan ba a manta ba, a wani babban taro na jam'iyyar APC, kwamitin ayyuka na jam'iyyar ya tsige Oshiomhole daga kujerar shugaba, bayan ya riƙe muƙamin daga 2018 zuwa 2020.

Tsige Oshiomhole daga ofis alhalin yana da ragowar shekaru biyu a gaba ya jawo cece-kuce, inda tsohon shugaban jam'iyyar, Ntufam Eta ya ce an yi haka don a hana Bola Tinubu takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ganduje na nan a matsayin shugaban APC na ƙasa bayan hukuncin kotu, bayanai sun fito

"Babu hurumin tsige Ganduje" - Morka

Amma a kan lamarin tsige Ganduje, Mr. Morka ya ce wadanda ke hanƙoron an kore shi ba halastattun 'ya'yan jam'iyyar bane.

"Shi Oshiomhole halastattun'ya'yan jam'iyyar ne suka taru suka tsige shi, amma Ganduje wasu bara-gurbi ne suka aikata hakan, kenan akwai banbanci a tsakaninsu.
"Muna so mu kara tabbatar wa duniya cewa wadanda suka fara kitsa batun tsige Ganduje daga jihar Kano ba mu sansu ba, basu da wani hurumi na tsige shugaban jam'iyyar."

- A cewar Morka.

"Har yanzu Ganduje ne shugaba" – APC

Morka ya kuma ce har yanzu tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ne shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Jaridar Vanguard ta rahoto Morka ya ce jam’iyyar ba za ta mutunta umarnin kotu na farko da ya tabbatar da dakatar da Ganduje a matsayin shugabanta na kasa ba.

Har yanzu ni ne shugaban APC - Ganduje

Kara karanta wannan

'Babu wanda zai shigo APC sai da izinin Ganduje,' An ja kunnen Kwankwasiyya

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa Abdullahi Ganduje ya yi wa gwamnatin jihar Kano shagube da cewar "kujerar APC tana kan Ganduje ne, kuma zama daram dam."

Ganduje ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne ya tabbatar masa da shugabancin APC, yayin da ake ta takaddamar tsige shi daga kujerarsa ta shugaban jam'iyyar na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.