Dalilin dakatar da Oshiomhole daga shugabancin APC na kasa
Wata babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Mai shari’a Danlami Senchi a ranar Laraba, ya ba Oshiomhole umarnin ya daina kiran kansa da shugaban jam’iyyar ta kasa har sai lokacin da aka kammala shari’ar da ta ke bukatar tumbuke shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC din.
Kotun ta bada umarnin ne bayan ta samu korafi a ranar 16 ga Janairu na Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso gabas; Anselm Ojezua, shugaban jam’iyyar na jihar Oyo da wasu mutane hudu.
Korafin anyi shi ne a kan Oshiomhole, jam’iyyar APC, sifeta janar din ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar tsaro ta fararen kaya (SSS).
Ta hannun lauyansu, Oluwole Afolabi suka bukaci kotun da ta hana Oshiomhole bayyana kansa ko yin wasu aiyuka da zasu nuna shi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa baki daya har sai lokacin da shari’ar ta kammala.
Sun kara da bukatar kotun da ta hana Oshiomhole yanke wani hukunci a matsayin shugaban jam’iyyar APC din na kasa tare da hana shi shiga ofishinsa har sai an kammala shari’ar.
Sun kara da bukatar kotun da ta umarci sifeta janar da kuma jami’an tsaron farin kaya da su tura jami’ansu don mamaye ofishin shugaban jam’iyyar APC din na kasa, tare da hana shi shiga har sai an kammala shari’ar.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad
Afolabi ya sanar da kotun cewa ko baya da jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da Oshiomhole, bai kalubalanci hakan ba. Ya ce amsar bukatar na da matukar amfani idan aka duba irin rashin da jam’iyyar tayi a jihohin Zamfara, Ribas da Bayelsa.
A yayin yanke hukunci a ranar Laraba, Mai shari’a Senchi ya karba dukkan bukatun masu korafin. Ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 da kuma 8 ga watan Afirilun 2020.
Da farko dai kotun tayi watsi da bukatar hukumar jami’an tsaro ta farin kaya. wacce ta bukaci a tsameta daga wannan koken.
Mai shari’ar ya bayyana cewa an saka sifeta janar din ne da hukumar jami’an tsaron ta fararen kayan don su tabbatar da wanzuwar hukuncin kotun.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng