Matatar Dangote Ta Rage Farashin Mai Ne Saboda Rashin Inganci? Gaskiya Ta Fito
- Matatar man Aliko Dangote ta ƙaryata rade-radin cewa ta rage farashin dizal ne saboda rashin ingancin kayanta
- Kamfanin ya yi wannan martanin ne yayin da ake yaɗa jita-jitar cewa man da take samarwa ba shi da inganci sosai
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai siyar da mai a jihar Taraba kan yanayin man dizal na Dangote da ake magana a kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Hukumomi a matatar man Aliko Dangote sun yi martani kan jita-jitar samar da man dizal wanda ba ingantacce ba.
Matatar ta yi fatali da rade-radin inda ta ce babu kamshin gaskiya a labarin da ake yaɗawa kan haka, cewar Leadership.
Wane martani matatar Dangote ta yi?
Ta ce an kirkiri labarin ne domin biyan buƙatar wasu inda ta ce ta na samar da ingantaccen man dizal wanda ya ke da ƙarko dai-dai da kasuwannin duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martani ya biyo bayan zargin cewa man ba shi da inganci wanda ake ganin dalilin haka ne ya saka matatar rage farashi.
Kakakin matatar, Anthony Chiejina shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, cewar rahoton Arise News.
Anthony ya ce an kirkiri labarin karya ne kawai domin bata sunan kamfanin inda aka yada cewa suna saka sinadarin 'Sulphur' da yawa.
Ta bayyana musabbabin rage farashin
"Zargin cewa matatar Dangote na samar da man dizal marar inganci kwata-kwata ba gaskiya ba ne."
"Zargin cewa sinadarin 'Sulphur' ya yi yawa a cikin shi yasa ma aka rage farashin da kaso 37 ba gaskiya ba ne."
"Abin da muke samarwa ya kai kaso 80 mafi kyau fiye da ingancin wanda ake shigo da shi Najeriya."
- Anthony Chiejina
Chiejina ya ce dalilin rage farashin bai rasa nasaba da yawan tururuwa da ake yi neman dizal a kamfanin da kuma yanayin sauye-sauyen kasuwa.
Martanin mai siyar da mai kan lamarin
Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai siyar da mai a jihar Taraba kan yanayin man dizal na Dangote.
Adamu Jibril da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba ya ce tabbas ya fuskanci matsala kan man dizal din.
"Gaskiya kam ina siyar da man a gidan mai kuma ni daman gas na ke siyarwa, gaskiya mun ɗauki tsawon lokaci bama kawo wata kalar dizal sai mai haske."
"To a wannan lokaci sai aka kawo mana dizal din sai naga ya na da duhu kaman ruwan zuma kuma haka na ke siyarwa har kwanaki uku sai wasu masu babbar mota suka ce gaskiya wannan gas ba shi da kyau ya na bata musu mota."
"Wasu kuma za su zo siya sai su ce basu son irin wannan dizal din sai idan ba wani ba yadda suka iya sai su siya wannan din, amma dai wasu basu korafi."
- Adamu Jibril
Tinubu ya yabawa Dangote kan rage farashi
A baya, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa Aliko Dangote kan rage farashin litar dizal a matatarsa.
Tinubu ya ce tabbas wannan mataki zai taimaka wurin inganta tattalin arzikin Najeriya da kuma ba da damarmaki ga 'yan ƙasar.
Asali: Legit.ng